Home Labarai Ba mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba – Gwamnatin Najeriya

Ba mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba ta taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba ko nuna wariyar addini ba, bayan rahoton bincike kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci da Majalisar Wakilan Amurka ta fitar.

Gwamnatin ta ce “duk da ƙalubalen tsaro da wasu yankuna ke fuskanta, matsalolin sun samo asali ne daga ta’addanci da fashi da makami, da rikice-rikicen al’umma.”

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitr a ranar Talata, inda ya ce ƙundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadi ‘yancin addini da ibada ga kowane dan kasa, kuma gwamnati na nan daram wajen kare waɗannan haƙƙoƙi da tabbatar da adalci ga kowa.

Ministan ya ƙara da cewa “gwamnati ta ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwar jami’an tsaro a yankunan da matsalar ta fi ƙamari, tare da fadada farmakin yaki da ta’addanci da lalata hanyoyin masu garkuwa da mutane, da kuma kama manyan masu aikata laifi.”

Haka kuma gwamnatin Najeriya ta inganta haɗin gwiwar hukumomi domin saurin ɗaukar mataki musamman a yankunan karkara masu rauni in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, tana mai cewa ƙasar na maraba da tattaunawa da haɗin kai bisa mutunta juna da mutunta ikon ƙasashe.

Ta ce gwamnati za ta ci gaba da aiki da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa ta hanyoyin diflomasiyya yayin da take mai da hankali kan babban nauyinta na kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan kasa.

A jiya ne ƴan majalisar wakilan Amurka suka gabatar da rahoto ga shugaban Amurka Donald Trump kan binciken da suka kammala game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp