Fiye da Kashi 60 na ‘Yan Najeriya a Yanzu Suna Rayuwa Cikiin Fatara – IMF
Asusun Lamuni na Duniya ya ce garambawul ɗin da gwamnatin Najeriya ta aiwatar ya ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar, amma ya yi gargaɗin cewa fiye da kashi 60 na ‘yan Najeriya a yanzu suna rayuwa cikiin fatara.
Tun bayan hawansa kan mulki shekara uku da ta wuce, Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur mai tsada wanda ya sa tsawon shekaru gommai ‘yan ƙasar ke shan man fetur da arha, sannan ya sassauta tsarin canjin kuɗi ga naira kuma ya yi wa harkar karɓar harajin Najeriya gyaran fuska.
Read Also:
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito IMF na cewa yayin da masana tattalin arziƙi ke cewa ya dace a kawo manufar sauye-sauyen tun da daɗewa, amma talauci ya ci gaba da ƙaruwa, inda a ƙarshen shekara ta 2025 yake addabar kashi 63 na al’ummar Najeriya.
Kuma sama da mutum miliyan 27 ne ke fama da rashin wadatar abinci a shekarar, in ji IMF.
A cikin wata sanarwa bayan bitar tattalin arziƙin najeriya na shekara-shekara, IMF ya ce: “Har yanzu halin rayuwa ya kasance mai wahala ga ‘yan Najeriya masu yawa”.
Ya ce talauci na ƙaruwa a ƙasar mafi yawan jama’a a Afirka tsawon shekaru, inda rahoton Babban Bankin Duniya na baya-bayan nan ya ce ‘yan Najeriya kimanin kashi 61 ne ke rayuwa cikin talauci, sama daga kashi 40 na adadinsu a 2019.












