Majalisar Wakilan Najeriya ta Amince da ƙudirin Dokar Kafa ’Yan sandan Jiha
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis ta amince da ƙudirin gyaran tsarin mulki wanda ke neman kafa rundunar ’yan sandan jiha a faɗin ƙasar.
Kudirin, mai taken “ƙudirin Dokar Gyaran Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 don samar da Rundunar ’Yan sandan Jiha da sauran al’amura masu alaƙa da hakan (Gyara na Shida), na shekarar 2026,” an amince da shi ne yayin tattaunawa a babban zauren majalisar.
ƙudirin ya tsallake matakin ne bayan da mambobin majalisar suka kaɗa masa ƙuri’a da gagarumin rinjaye biyo bayan gabatar da rahoton da Mataimakin Shugaban Majalisar, kuma Shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulki na Majalisar, Benjamin Kalu ya yi.
Read Also:
Hanyar kaɗa ƙuri’a da hannu da majalisar ta yi ta nuna cewa ’yan majalisa 289 ne suka goyi bayan shawarar, mamba guda daya ya ƙi kaɗa ƙuri’a, yayin da babu ko da ɗan majalisa guda da ya ƙeƙashe ƙasa ya ki amincewa da shi.
Gyaran da ake shirin yi yana neman samar da tsarin gudanar da aikin ’yan sanda guda biyu ne da ya ƙunshi ’Yan sandan Tarayya da na Jiha, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar ta hanyar amfani da raba madafun iko.
A ƙarƙashin shawarar, za a yi gyara ga Sashi na 214 na Tsarin Mulki domin kafa waɗannan rundunoni biyu na ’yan sanda a hukumance.
Majalisar Dokoki ta ƙasa za ta sami ikon ƙayyade tsari, gudanarwa, da kuma ikon ’Yan sandan Tarayya, yayin da kuma za ta gindaya sharuɗan da suka dace don kafa da kuma gudanar da ayyukan rundunonin ’yan sandan jihohi.












