Home Taska Ƴan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari’a da ke Jihar Katsina

Ƴan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari’a da ke Jihar Katsina

Ƴan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari’a da ke Jihar Katsina

 

Wasu ƴanbindiga sun kai hari a wata kotun shari’a da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya a ranar 29 ga Yuli, inda alƙalin kotun ya tsere kafin maharan su kutsa, kamar yadda Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 30 ga Yuli.

Mazauna yankin sun ce Alƙali Mohammed Muktar ya tsere ta taga bayan ya hango maharan na tunkarar kotun da ke ƙauyen Gwarjo a ƙaramar hukumar Matazu.

Wani mazaunin yankin ya ce: “Ƴanbindigar sun shiga cikin kotun suna harbe-harben kan mai uwa da wabi, kuma suna ta tambayar inda alƙalin yake. Amma sai ya samu nasarar tserewa ta taga, sannan wani ɗan acaba ya taimaka masa kafin su iso.”

Wani ganau ya kuma ce maharan sun yi barazanar kashe Alƙali Muktar idan har ya sake dkomawa domin sauraron shari’o’i.

Mazauna yankin na ganin cewa ‘yan bindigar sun zo ne domin kashe alƙalin ko kuma su yi garkuwa da shi domin neman kuɗin fansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp