Minista Sadiya Umar Farouq ta Jajantawa Waɗanda Gobarar Sansanin ‘Yan Gudun Hijira ta Shafa a Borno
Ministan Ma’aikatar kula da Al’amuran jin kai da sarrafa annoba da ci gaban al’umma, Ta jajantawa waɗanda gobarar ta shafa.
Maigirma Ministar ma’aikatar Al’amuran jin kai da sarrafa annoba da ci gaban Al’umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana bakin cikinta kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna El-Badawy, da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da babban sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alkali ya fitar.
Ministar ta jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a gobarar.
Read Also:
A bayanin nata ministar ta kara da cewa, “Rahotannin da suka iso gare ni sun tabbatar da asarar rayuka, an kuma samu lalacewar matsugunai dubu uku (3,000).
Don haka Ministar tace, yawaitar barkewar gobara a Sansanonin ‘Yan gudun hijirar abin damuwa ne kuma Gwamnatin Tarayya da Hukumomin da abin ya shafa a Jihohin za su dauki matakan dakile afkuwar lamarin nan gaba.
A halin da ake ciki, Ministar tace “Na umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa da ta gaggauta aika kayan agaji ga wadanda abin ya shafa a sansanin, yayin da za a gudanar da tantance musabbabin gobarar da ma irin barnar da ta yi.
” Mai girma ministar tayi kira ga mutanen da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijiran da su yi taka-tsan-tsan don hana afkuwar barkewar gobara.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 39 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 20 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com