Rikicin Rasha da Ukraine: ‘Yan Najeriya Sun Roki Shugaba Buhari ya Gargadi Minista Lai Mohammed ya Kame Bakinsa Game da Lamarin
Ma’abota amfani da dandalin sada zumunta a Najeriya sun roki gwamnatin tarayya ta rufa wa kasar asiri ta yi shiru game da yakin Rasha da Ukraine.
Mutane da dama a dandalin sada zumuntan sun nuna fargabarsu kan abin da ka iya faruwa idan Najeriya ta tsoma bakinta duba da irin barazanar da Putin ya yi wa Amurka da NATO.
Wasu masu tsokacin sun roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi Minista Lai Mohammed ya kame bakinsa game da lamarin idan ba haka ba su bar kasar.
Wasu yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta sun shawarci gwamnatin tarayya ta ja bakinta ta yi shiru game da yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, rahoton Vanguard.
Hakan na zuwa ne bayan Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gargadi Amurka da NATO idan suka saka baki, ‘Rasha za ta mayar da martani nan take, kuma za ku fuskanci sakamakon da ba ku taba samu ba a tarihin ku.’
Read Also:
A lokacin hada wannan rahoton, kimanin sojojin Ukraine 137 ne suka mutu tun bayan da Rasha ta fara kutsa wa Ukraine a safiyar ranar Alhamis, sannan sojoji 316 sun jikkata.
Ga abin da wasu yan Najeriya ke cewa kamar yadda Vanguard ta tattaro:
Folorunsho Akin-Martins Odeyemi cewa ya yi:
“Ba na tunanin komai, kada dai gwamnatin mu ta saka baki domin Kawu Putin ainihin dan kungiyar asiri ne.”
Vincent John Ajakaiye ya ce:
“Don Allah wani ya shawarci Lai Mohammed kada ya ce komai domin idan ya yi magana zan kwashe kaya na in tafi Burkina-Fso domin samun zaman lafiya a rayuwa ta.”
Nkeiruka Best cewa ta yi:
“Ba mu gama tunanin yunwa da ke damun mu ba kuna son ku kara tunanin matsalar Rasha da Ukraine …
ko dai ba ku san abin da ya faru da mutumin farko da ya saka bakinsa a abin da babu ruwansa ne … idan kun ga dama su saka shugaban mu ya tsoma baki, za ku ji a jikinku.”
Shi kuma Okoro De MoneyMaker ya ce:
“Don Allah Buhari, saboda Najeriya ka fada wa Lai Mohammed kada ya yi tsokaci a kan wannan lamarin.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 50 minutes 26 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 31 minutes 51 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com