PDP Zuwa APC: Kotu ta Dage Zaman Shari’a Kan Sauya Shekar Gwamnan Jahar Cross River
Babban kotun tarayya dake Abuja ta dage zaman shari’a kan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar na kwace kujerar Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade da mataimakinsa, Ivara Esu.
Jam’iyyar hamayyar ta shigar da karar ne saboda sauya shekarsu zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC).
An shirya zama yanke hukunci kan lamarin yau amma Alkali Taiwo Taiwo ya dage zaman zuwa ranar 6 ga Afrilu, 2022, rahoton ChannelsTV.
Read Also:
Abinda ya fadawa yan majalisa ka iya fadawa kansa
Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta sallami wasu mambobin majalisar dokokin jihar Cross River su 20 a ranar Litinin, 21 ga watan Maris.
Kotu ta kwace kujerun su ne saboda sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke, ya riki cewa ya zama dole yan majalisar su sauka daga kujerunsu kasancewar sun yi watsi da jam’iyyar da ta dauki nauyin kawo su kan mulki.
Hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/975/2021, da PDP ta shigar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 34 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 15 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com