• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Taska ‘Yan Bindiga na ci Gaba da Kai Farmaki Jahar Neja
  • Taska

‘Yan Bindiga na ci Gaba da Kai Farmaki Jahar Neja

By
Ozumi Abdul
-
February 13, 2022
Arewa Award

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Neja.

An tattaro cewa harin wanda suka fara kaddamarwa a yammacin ranar Asabar yana nan yana ci gaba da gudana har yanzu haka.

Shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Ibeto, ya tabbatar da hare-haren.

Neja – ‘Yan bindiga na ci gaba da kai farmaki a garuruwan Zoma, Yangalo, Masamagu, Atabo da sauran garuruwan da ke makwabtaka a karamar hukumar Magama ta jihar Neja.

Mummunan harin ya tursasa mazauna kauyukan tserewa zuwa garin Kontagora, hedikwatar karamar hukumar Kontagora.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa farmakin wanda suka fara kaiwa a yammacin ranar Alhamis na ci gaba da gudana har yanzu haka, inda aka ce mutane da dama sun mutu sannan an yi garkuwa da wasu da dama.

Har ila yau rahoton ya nuna cewa wasu da dama sun jikkata a harin yayin da wasu suka tsere daga gidajensu.

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin sake kira amma zuwa yanzu bai aikata hakan ba.

Sai dai shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Ibeto, ya tabbatar da hare-haren.

Read Also:

  • Gwamnan Kano ya aikewa Majalisar dokoki sunan wanda zai shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa
  • Tinubu ya yi karin wa’adin Aiki ga shugaban Custom na Nijeriya
  • Gini kan magudanan ruwa ne ya haifar da Ambaliyar Maiduguri

Wasu mazauna kauyukan da suka zanta da Daily Trust a ranar Lahadi, 13 ga watan Fabrairu, sun ce maharani suna ta kai hari tun daga ranar Alhamis ba tare da hukumomin tsaro sun shiga lamarin ba.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Ko da muka fara masu, basu kawo dauki ba. An barmu a hannun yan bindiga.”

Wata dattijuwar mata, Khadijah Abdullahi, ta ce yaranta aurarru mata su biyu wadanda ke da yara biyar da uku na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Wata da ta tsallake rijiya da baya a harin, Safiya Abdullahi, ta ce:

“Da na hango su, sai na gudu na haye kan tsauni. Ban san cewa wasu daga cikinsu sun gan ni ba lokacin da nake boyewa. Na lullube kaina da hijabi. Suna a kan kimanin babura 30. Cikin ikon Allah, sai suka bukaci na gaggauta barin wajen. Ta haka ne na tsira.”

Wani da ya tsere, Shamsudeen Abdulmalik Atabo, ya ce maharani sun fara kai hari a garuruwa uku da misalin 12:00 na rana kuma har zuwa yammacin Asabar suna chan.

“Matar yayana na cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Yanzu haka ina a Kontagora inda nake zama tare da yan uwana.”

Daily Trust ta tattaro cewa har yanzu yan bindigar na nan suna kai hari a Yangalo, babban garin da suka tara dabobbin sata. Mazauna kauyukan da suka tsere suna samun mafaka a Usubu, wani yanki na Kontagora.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • 'yan bindiga
  • Farmaki
  • Neja
Previous article2023: Wannan Lokacin ne da Arewa za su Nuna Goyan Baya ga Tinubu – Kashim Shettima
Next articleAbubuwa 5 game da Sheikh Ahmad Gumi
Ozumi Abdul

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP

Magance Karancin Naira: CBN ya Umarci Bankuna da su yi Aiki a Ranakun Asabar da Lahadi

Hatsarin Mota ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 25 a Bauchi

Hukumar NITDA ta Gabatar da Satifiket ga Matan da Suka Samu Horo Kan Fasahar Zamani

Ambaliyar Ruwa a Jigawa: Gidauniyar Ƙasar Qatar da ta Malam Inuwa Sun Raba Tallafin Abinci ga Mutane 1,000

An Gudanar Da Bikin Arewa Stars 30 Under 30 2022, Cikin Nasara

Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago

‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Kashe ‘Yan Sanda Biyu a Anambra

Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

Gidauniyar Malam Inuwa ta Ɗauki Nauyin Koyar da Ƴa’yan Fulani Al-ƙur’ani

Bincike: Shin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ƙirƙiro da Tambayoyi Domin Tantance kungiyoyin Musulmi da Kirista a kidayar 2023? 

Recent Posts

  • Gwamnan Kano ya aikewa Majalisar dokoki sunan wanda zai shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa
  • Tinubu ya yi karin wa’adin Aiki ga shugaban Custom na Nijeriya
  • Gini kan magudanan ruwa ne ya haifar da Ambaliyar Maiduguri
  • KACHMA ta yabawa KAROTA bisa inganta lafiyar Jami’anta
  • Dino Melaye ya koma jam’iyyar ADC bayan ficewarsa daga PDP

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1506 days 8 hours 31 minutes 2 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1488 days 10 hours 12 minutes 27 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Gwamnan Kano ya aikewa Majalisar dokoki sunan wanda zai shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawaTinubu ya yi karin wa'adin Aiki ga shugaban Custom na NijeriyaGini kan magudanan ruwa ne ya haifar da Ambaliyar MaiduguriKACHMA ta yabawa KAROTA bisa inganta lafiyar Jami'antaDino Melaye ya koma jam'iyyar ADC bayan ficewarsa daga PDPMamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a MaiduguriAn samu raguwar hare-haren Boko Haram da na ƴan bindiga - RibaduHadarin jirgin ruwa yayi sanadin mutuwar mutum 6 a jihar JigawaZanga-zanga ta barke a sansanin ƴan gudun hijra mafi girma da ke Kenyazamu hallaka Da;iban da ke hannun mu matukar baku biya Fansa ba - 'Yan BindigaGwamnan Zamfara ya Amince da Nadin Sabon Sarki GusauAkalla jami'an tsaron jihar Katsina 100 suka mutu a bakin aiki - KwamishinaYadda yan bindiga suka yiwa mutane 38 yankan RagoAmbaliyar ruwa ta lalata gidaje tare da kashe mutane 23 da a birnin YolaFadar shugaban Kasa ta magantu kan zargin da Kwankwaso ya yiwa Tinubu
X whatsapp