Aljeriya Za ta Fara Biyan Matasa Marasa Aikin yi a Fadin Kasar
Shugaban Aljeriya ya ce zai ɓullo da tsarin biyan matasan da ba su da aikin yi a ƙasar yayin da take fama da adadin marasa aikin.
Read Also:
Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya faɗa wa ‘yan jarida cewa za a fara biyan matasan ‘yan shekara 19 zuwa 40 daga watan Maris.
Waɗanda suka cancanci shiga tsarin za su karɓi kuɗin da ya kai kusan dala 100 duk wata, da kuma wasu tallafi na lafiya, har sai sun samu aikin yi.
Da yake ba da sanarwar, Mista Tebboune ya ce Aljeriya ce ƙasa ta farko da ta fito da irin wannan shiri wadda ba ta Turai ba.
Ya ƙara da cewa akwai marasa aikin yi 600,000 a ƙasar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 53 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 34 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com