Home Taska Faɗawa Cikin Rijiya: Mutane 13 Sun Rasa Rayukansu Ana Tsaka da Shagalin...

Faɗawa Cikin Rijiya: Mutane 13 Sun Rasa Rayukansu Ana Tsaka da Shagalin Biki a Indiya

Captured Boko Haram spies by troops
Captured Boko Haram spies by troops

Faɗawa Cikin Rijiya: Mutane 13 Sun Rasa Rayukansu Ana Tsaka da Shagalin Biki a Indiya

Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu bayan sun fada cikin wata rijiya yayin wani biki da ake yi a jihar Utter Pradesh da ke yammacin Indiya.

Yan sanda sun ce wadanda abin ya ritsa da su – duka mata ne da yara – na zaune kan murfin da aka rufe rijiyar da shi a lokacin da ya rufta saboda nauyin mutanen da ke kansa.

Lamarin ya faru ne ranar Laraba da yamma a lokacin bikin gargajiya na “haldi”, inda ‘yan uwa suke shafa wa ango da amarya ruwan kurkur a fuska a matsayin alamar samun wadata.

Wasu karin mutum biyu sun jikkata a hatsarin, wanda ya faru a gundumar Kushinagar.

Firaminista Narendra Modi ya bayyana mutuwar tasu a matsayin “mai sosa zuciya”.

Lokacin da murfin ya karye, sauran baki sun ruga don ceto mutanen, inda suka kai su wani asibiti da ke kusa. Yayin da aka sanar da mutuwar mutum 11 nan take, wasu biyu kuma sun mutu a asibit, in ji ‘yan sanda.

Babban Ministan Utter Pradesh Yogi Adityanath ya nemi shugabannin ananan hukumomi da su taimaka wa iyalan mutanen da abin ya ritsa da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp