Rikicin Ukraine da Rasha: ‘Yan Wasan Brazil Sun Roki Gwamnatin Kasarsu da ta Taimaka ta Kwashe su Daga Ukraine
Yan wasan Brazil da ke wasa a kungiyoyin Shakhtar Donetsk da Dynamo Kyiv sun roki gwamnatin kasarsu da ta taimaka ta kwashe su daga Ukraine.
Hakan ya biyo bayan hare-haren da Rasha ta fara kai wa Ukraine da safiyar Alhamis.
Wasu daga cikin yan wasan sun yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda suka bayyana halin da suke ciki tun bayan barkewar rikicin, da kuma bukatar hukumomin Brazil su taimaka su kwashe su tare da iyalansa daga Ukraine.
Read Also:
Dan wasan gaban Shakhtar Donetsk Junior Moraes ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa ”halin da muke ciki ya yi muni. Ina so al’umma su yada wannan bidiyo har sai ya kai ga hukumonin Brazil.”
Ya kara da cewa ”an rufe kan iyakoki da bankuna, babu man fetur, kuma za a fuskanci karancin abinci da kudade a hannun jama’a.”
” Yan uwa da abokan arziki yanayin da muke ciki ya yi muni don mun makale a Kyiv muna neman mafita. Yanzu haka muna cikin wani otal ne. Ku taya mu da addu’a.” In ji Moraes.
Akwai akalla yan wasan Brazil 12 da ke wasa a kungiyar kwallon kafa ta Shakhtar, da suka hada da David Neres wanda bai dade da zuwa kungiyar ba daga Ajax da ke Holland.
Sauran yan wasan sun hada da Dodo, da Vitao, da Marlon, da Ismaily, da Vinicius Tobias, da Maycon, da Marcos Antonio, da Tete, da Alan Patrick, da Pedrinho da kuma Fernando.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 31 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 12 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com