Home WASANNI Kasuwar ‘Yan ƙwallo: Kocin PSG Mauricio Pochettino ya yi Watsi da Bukatar...

Kasuwar ‘Yan ƙwallo: Kocin PSG Mauricio Pochettino ya yi Watsi da Bukatar Manchester United

Kasuwar ‘Yan ƙwallo: Kocin PSG Mauricio Pochettino ya yi Watsi da Bukatar Manchester United

Paris St-Germain na iya mika tayi kan ɗan wasan Chelsea mai shekara 30 da ke buga tsakiya dan asalin Faransa, N’Golo Kante, a wannan kakar. (Telegraph)

Kocin PSG Mauricio Pochettino, mai shekara 49, ya yi watsi da bukatar Manchester United ta komawa Old Trafford yayin da yake jiran damar tafiya Real Madrid. (Sport – via Star)

Ɗan wasan Ingila mai shekara 28, Harry Kane, na iya sake gabatar da bukatar barin Tottenham idan kocinsu Antonio Conte ya ajiye aiki a Spurs. (Express)

Georginio Wijnaldum na Netherlands mai yiwuwa ya yi bankwana da PSG bayan zaman kaka guda, ana dai alakanta tsohon dan wasan na Liverpool da Atletico Madrid, West Ham, Newcastle United da Aston Villa. (Calciomercato – in Italian)

Arsenal ta tuntubi wakilan Alexander Isak sai dai tana son Real Sociedad ta rike kudaden da ta nema kan ɗan wasan mai shekara 22 kafin a cimma yarjejeniya. (Sport, via Mail)

Chelsea na duba yiwuwar tsawaita zaman ɗan wasanta Cesar Azpilicueta a kungiyar wanda ke karewa a wannan kakar, sai dai ɗan wasan mai shekara 32 na son kungiyar ta yi nazarin irin tayin da yake samu daga wasu kulob din kafin yanke hukunci a kansa. (90min)

Mai bugawa Manchester United tsakiya Paul Pogba ɗan shekara 28 ya ce a shirye yake ya koma Paris St-Germain, a cewar tsohon ɗan wasan Chelsea Nicolas Anelka. (RMC Sport, via Star)

Ɗan wasan RB LeipzigAngelino na iya bankwana da ita nan kusa, akwai da irinsu Arsenal, Tottenham da Barcelona da ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 25. (Calciomercato – in Italian)

Southampton na fatan iya sake sabunta zaman ɗan wasanta mai shekara 19 Tino Livramento ko da na kaka guda ne, yayin da Manchester United ke matsawa kan saye shi. (Sun)

Abokan hamayya a Landan West Ham da Brentford na zawarcin ‘yan wasan Hull Citybiyu, Keane Lewis-Potter da Jacob Greaves, duk masu shekara 21. (90min)

Mai tsaron baya a Denmark Andreas Christensen bai zai koma wata ƙungiyar Firimiya ba, saboda girmamawar da ya ke yi wa Chelsea idan kwantiraginsa na ya kawo karshe a Stamford Bridge. Barcelona da Bayern Munich na zawarcinsa. (Fabrizio Romano)

West Ham, Leicester City da Everton sun kasance kungiyoyin da aka ce sun kwadaitu da ɗan wasan Bristol City mai buga tsakiya Alex Scott, ɗan wasan mai shekara 18 na jan hankalin kungiyoyi ketare. (Mail)

Aston Villa a shirye take ta gabatar da tayi kan tsohon ɗan wasan da ke buga ajin ‘yan kasa da shekara 21 a Ingila mai shekara 24 Ezri Konsa. (Football Insider)

Atletico Madrid na duba yiwuwar saye ɗan wasan Napoli Giovanni di Lorenzo, ɗan shekara 28. (Diario AS – in Spanish)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp