Yadda Mai Shayi ya Halaka Kwastoman sa Saboda N10 a Jahar Ogun
Wani mai shayi mai suna Hamidu, yana hannun hukuma bayan ya halaka wani kwastoman shi a anguwar Arepo, karkashin karamar hukumar Obafemi Owode cikin Jihar Ogun.
An samu bayanai akan yadda kwastoman, mai suna Musa ya siya shayin N50 a wurin Hamidu ya biya shi N40, yayin neman cikon kudin, rikici ya barke tsakanin su.
Hamidu ya ka wa Musa naushi a kirji daga nan Musa ya fadi ba tare da ya shura ba, ya koma ga mahaliccin sa take anan hakan yasa aka kira ‘yan sanda suka wuce da Hamidu.
Jihar Ogun – Wani Hamidu mai shayi ya halaka kwastoman sa mai suna Musa akan N10 a anguwar Arepo da ke karkashin karamar hukumar Obafemi Owode cikin Jihar Ogun.
The Punch ta tattaro bayanai akan yadda Musa ya siya shayi a hannun Hamidu, maimakon ya biya shi N50 sai ya ba shi N40.
Saboda amsar cikon kudin ne rikicin ya barke musu suka dinga ba hammata iska.
Read Also:
Hamidu ya yi gaggawar naushin Musa a kirji wanda ya sa ya fadi kasa warwas.
Shugaban Odua People’s Congress (New Era), Olayiwola Ogunsolu ya sanar da wakilin The Punch yadda Musa ya mutu take yanke.
Yadda lamarin ya auku
Kamar yadda ya ce:
“Ranar Larabar da ta gabata, muna kasan gadar Arepo inda muka ji hayaniya wuraren anguwar Hausawa.
“Bayan isar mu wurin muka ga gawar mutumin. Bayan tambayar yadda lamarin ya auku, an sanar da mu cewa mai shayi ne ya halaka shi akan ya ki biyan N50 na kudin kofin shayi.
“Mun yi gaggawar sanar da ‘yan sanda wadanda suka zo suka wuce da mai shayin.”
Dan uwan mamacin ya shaida yadda Musa ya biya N40 maimakon N50 wanda hakan ya hassala mai shayin har ya yi masa aika-aikar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce bai san komai dangane da lamarin ba
Shugaban Hausawa yankin, Usman Shehu ya ce bai san komai ba dangane da lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya yi alkawarin sanar da wakilin The Punch idan ya samo bayanai.
Har aka kammala rubuta wannan rahoton bai tuntube shi ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 35 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 17 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com