Abubuwa 5 da Kuke Bukata Kafin Shiga Aikin Soja a Najeriya

Abubuwa 5 da Kuke Bukata Kafin Shiga Aikin Soja a Najeriya

 

Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwar daukar sabbin ma’aikata na shekarar 2022/2023.

An nemi wadanda ke da sha’awar shiga aikin soja su ziyarci shafin rundunar na yanar gizo don cike fom.

A nan, mun tattaro wasu abubuwa biyar da dole sai me neman aikin ya cike su

A ranar Talata, 8 ga watan Maris ne, rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewar shirinta na daukar ma’aikata na 2022/2023 na gudana a yanzu haka.

An bukaci wadanda ke sha’awar aikin da su ziyarci shafin daukar aiki na rundunar sojin domin ganin yadda za su nemi aikin, Daily trust ta rahoto.

Idan kana son shiga aiki soja, dole ka cike wadannan abubuwan bukata:

1. Dole ka kasance dan Najeriya sannan ka mallaki katin shaida na dan kasa.

2. Dole ka mallaki akalla kredit 5, ciki harda Ingilishi a jarrabawar WASSCE, GCE, NECO ko NAPTIB a zama da bai wuci biyu ba.

3. Dole mutum ya kasance da lafiyar jiki da na kwakwalwa kuma kada mutum ya yi kasa da mita 1.68 ga maza ko kuma 1.62 ga mata.

4. Dole mutum ya kasance tsakanin shekara 18 da 26.

5. Dole ne a cire fom din da aka cike ta yanar gizo, a sanya hannu akai sannan a zo dashi cibiyar jarrabawa yayin da aka fara tantance wadanda za su shiga aikin

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 59 minutes 15 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 40 minutes 40 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here