‘Yan Bindiga Sun Kai wa Tawagar Motocin Mataimakin Gwamnan Jahar Kebbi Hari

‘Yan Bindiga Sun Kai wa Tawagar Motocin Mataimakin Gwamnan Jahar Kebbi Hari

Yan bindiga sun farmaki tawagar motocin mataimakin gwamnan jihar Kebbi yayin da yaje ta’aziyyar kashe mutane a Kanya.

Rahoto ya nuna cewa jami’an tsaron dake tare da shi sun yi batakashi da maharan, kuma ɗan sanda mai mukamin ASP ya rasu.

Sakataren hulɗa da jama’a na mataimakin gwamnan yace Allah ya tseratar da maigidansa amma ya rasa mutum ɗaya.

Kebbi – Tsagerun yan bindiga sun farmaki jerin gwanon motocin mataimakin gwamna jihar Kebbi, Samaila Yombe, ranar Talata da daddare.

Vanguard ta tattaro cewa yan ta’addan kai wa tawgaar mataimakin gwamnan hari ne tsakiyar kauyen Kanya da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

A cewar sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan, Abdullahi Yalmo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’in ɗan sanda ASP Idris Umar Libata, ya rasa rayuwarsa.

Ya ce ɗan sandan ya rasa rayuwarsa ne yayin da suka tarbi yan bindigan, suka yi musayar wuta tsakanin su.

Daga ina mataimakin gwamnan ya fito?

Yalmo ya yi bayanin cewa uban gidanasa tare da rakiyar kwamandan barikin sojojin Najeriya dake Zuru na kan hanyar zuwa ta’aziyya da jaje ga iyalan mutanen kauyen na Kanya.

Mataimakin gwamnan yaje ta’aziyya ne biyo bayan wani mummunan lamarin da ya faru da harin yna bindiga, wanda ya lakume rayukan aƙalla yan Bijilanti 68, da kuma wasu fararen hula da dama.

Sakataren watsa labaran mataimamin gwamnan yace:

“Allah ya tseratar da Uban gidan mu, amma bisa rashin sa’a ya yi rashin ɗaya daga ciki haziƙan yan sandan take tare da shi.”

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sanda reshen jihr Kebbi, SP Nafiu Abubakar, bai ɗaga kiran wayar da aka jera masa ba domin tabbatar da abin da ya auku.

Yadda lamarin ya faru Labaran Magaji, ɗan asalin garin Danko Wasagu, ya shaida wa jaridar Premium Times cewa yan bindiga sun farmaki kauyen Kanya tun ƙarfe 5:00 na yamma.

Ya ce:

“Sun ci karfin jami’an tsaron, saboda sun yi gumurzu tun karfe 5:00 na yamma har zuwa karfe 8:00 na dare. Ikon Allah kawai ya tseratar da mataimakin gwamnan, yayin da jami’an tsaro suka tsaya kokarin dakile harin.”

“In banda wasu dakarun sojoji da suka kawo ɗauki, da yan bindigan sun ci karfin kowa sun kashe mataimakin gwamnan.”

Ya ƙara da cewa bayan yan bindigan sun tafi ne karin sojoji suka iso suka bi bayan su, yayin da wasu kuma suka kwashe gawarwakin waɗan da suka rasu.

A cewar Magaji, sojoji 13 da kuma yan sanda shida dake cikin tawagar mataimakin gwamna ne suka rasa rayuwarsu.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 40 minutes 26 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 21 minutes 51 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here