Dakarun ‘Yan Sandan Jahar Kaduna Sun Kama ‘Yan Bindiga 200 da ‘Yan Fashi 20 a Faɗin Jahar
Rundunar yan sanda ta jihar Kaduna tace ta samu nasarar yin ram da yan bindiga 200, yan fashi 20 a faɗin jihar.
Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa hukumar ta kwato makamai da yawa duk a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Ya ce namijin kokarin da yan sanda suka yi tun bayan kama aikin kwamishina shi ne sanadin samun zaman lafiya a jihar.
Kaduna – Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna tace dakarunta sun samu nasarar damke mutum 200 da ake zargin yan bindiga ne da yan fashi da makami 20 tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Kakakin yan sanda na jihar, ASP Mohammed Jalige, shi ne ya faɗi haka a taron manema labarai a hedkwatar hukumar, ranar Laraba a Kaduna, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Jalige ya bayyana cewa hukumarsu ta kwato bindigun AK47 guda 18, Alburusai 2000 kala daban-daban, kananan bindigun hannu 10, Motoci 10, babura 9 da sauran makamai.
Read Also:
A kalamansa da Channels tv ta rahoto, kakakin yan sandan ya ce:
“Mun saba gana wa da ku lokaci bayan lokaci domin bayyana nasarorin da muka samu a yaƙi da ta’addancin yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran manyan laifukan da suka shafi al’umma.”
“Hukumar yan sanda a tsawon wannan lokacin da muke magana tana sane da tabarbarewar kalubalen da suka addabi jihar nan da suka haɗa da harin yan bindiga, garkuwa, fashi da makami, rikicin makiyaya da manoma.”
“Mun yi iyakar bakin kokari wajen magance waɗan nan matsaloli kuma sanadin haka ne aka samu zaman lafiyan da mutane ke jin dadi a yanzun.”
Jalige ya ƙara da cewa lokacin da sabon kwamishinan yan sanda na Kaduna, Mudassiru Abdullahi, ya kama aiki, watanni kaɗan da suka wuce, jihar ta fuskanci kalubalen tsaro mai tsanani.
“Bisa goyon baya da taimakon sufeta janar na yan sandan kasa, da gwamnatin Kaduna, dakarun yan sanda sun jajirce wajen daƙile kalubalen tsaro, wanda yanzu mutanen yankuna suka samu sa’ida.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 42 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com