Kotun Koli a Najeriya ta Tabbatar da Soke Rajistar Jam’iyyun Siyasa 22
Abuja Kotun koli a Najeriya ta tabbatar da hukuncin soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa 22 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi a shekarun baya.
Jam’iyyu 22 na daga cikin 74 da INEC ta soke rajistarsu a 2020 sakamakon rashin tabuka abin a zo a gani a zaben 2019, inji rahoton Leadership.
Mai shari’a Ejembi Eko na kotun koli ya yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke, wanda ya kalubalanci matsayar INEC na soke rajistar jam’iyyun.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mai shari’a Eko ya bayyana cewa, Kotun daukaka kara a karan kanta ta tabo batun rashin sauraron shari’ar adalci ga bangaren jam’iyyun 22 da aka soke, inda ta cimma matsaya ba tare da jin ta bakin wasu bangarori a kan lamarin ba.
A cewar mai shari’a:
“Wannan bukata da INEC ta nema ya dace kuma an amince da hakan. Hukuncin kotun da ke kasa an yi watsi da shi.”
Kotun kolin ta bayyana cewa kotun daukaka kara ya fitar da batun sauraron karar ne daga duban bukatar daukaka kara da jam’iyyun siyasa suka shigar amma ta ki yin abin da ya dace domin yin adalci ga wasu da lamarin ya shafa.












