Tsohuwar Ministar Buhari ta Bayyana Yadda ta Ci gaba da Rayuwa Bayan Badakatar kwalin NYSC
Kemi Adeosun ta bayyana irin halin da ta riski kanta a ciki bayan badakatar satifiket dinta.
Tsohuwar ministar ta bayyana cewa bayan afkuwar lamarin ta kan yi kuka a kullun kwanan duniya har tsawon watanni uku.
Ta ce ta shiga kuncin rayuwa ta yadda take jinta kamar a cikin mummunan rami ba tare da aiki ba.
Tsohuwar ministar kudi, Misis Kemi Adeosun, ta fito ta bayyana yadda ta ci gaba da rayuwa bayan badakatar kwalin NYSC.
Punch ta rahoto cewa Adeosun ta ce kullun sai ta yi kuka ba tare da aiki ba tsawon watanni uku.
Adeosun, wacce ta magantu a bikin cika shekaru 10 na taron mata wanda cocin the Jesus House Church, United Kingdom ta shirya, ta yi bayanin cewa ji tayi kamar ta fada cikin wani mummunan rami.
A cewarta, komai game da rayuwarta ya tsaya cak yayin da take fama da jin kunya, cin amana, bakin ciki da tozarta.
Ta ce:
“Wannan lokaci na rayuwa ya kasance mai matukar wahala a gare ni. Na je na shiga yanayi irin na Ngozi Okonjo-Iweala. Don haka, na sha caccaka tun daga ranar farko, yanayin yay i kamar abubuwa basa tafiya daidai. Kwatsam sai tattalin arziki ya fara inganta. Kamar na fara ganin sakamakon da ake so. Daga nan kuma sai ga wata badakalar takardar shedar ta zo. Kuma kafin in ankara komai ya juye. Kuma haka lamarin ya yi fice.”
Adeosun ta ce abun bakin ciki ne cewa bata iya fadin nata bangaren na labarin ba sannan dole ta yi murabus a lokacin da ta ga ba za ta iya jure lamarin ba.
Tsohuwar ministar ta ce:
Read Also:
“An haife ni kuma na tashi a Burtaniya; hakika gidan iyayena na a Landan. Ziyarar da na kawo Najeriya har na kai shekara 34 hutu ne, da bizan da na samu a fasfot dina na Burtaniya. Lokacin da na gama makaranta, a lokacin babu damar zama yar kasa biyu; Ko dai na yi watsi da zama yar kasar Burtaniya ko kuma in rike shi kuma in yi aiki a nan. Ban yi watsi da nawa ba. Na gama makaranta ina da shekaru 21 kuma na fara aiki a 22.
“Na samu fasfot dina na Najeriya na farko ina da shekaru 34 lokacin da na dawo nan da zama, akwai muhawara kan ko batun dokar NYSC ya shafe ni. Da na yi tambaya kan matsayina game da NYSC, sai aka sanar da ni cewa saboda tarihin wajen zamana kuma na fi shekaru 30, an dauke mani yin bautar kasa. Sai da wannan lamari ya zo ya faru, shine iya sanina.
“Bisa ga wannan shawarar tare da jagora da taimakon wadanda nake tunanin amintattun aminai ne, an tuntubi hukumar NYSC domin ta ba da shaidarta. Daga nan na karbi takardar shaidar da ake magana. Kasancewar ban taba yin aiki a NYSC ba, ban taba ziyartar harabar ko kuma na san ayyukansu ba, ba ni da wani dalili da zan yi zargin cewa takardar shaidar ba ta gaske bace.
“Hakika, na gabatar da wannan satifiket a Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta 2011 da kuma a shekarar 2015 don tantancewa na hukumar DSS da kuma Majalisar Dokoki ta Kasa don tantancewa. Na nemi shawarar shari’a kuma babu matsala zan iya samun takardar dauke mani zuwa NYSC.
“Na sha kunya sosai a wancan lokacin saboda ni madubin dubawa ce ga matasa. Don haka, Don haka, abin da ya faru ya watsar da darussan da na koya wa matasa na. Ina kuka a kullun tsawon watanni uku; Ban yi wa kowa ko kaina komai ba tsawon wadancan watanni. Kuka kawai nake yi, kuka, da kuka.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 9 hours 54 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 11 hours 36 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com