‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 40 a Harin da Suka kai Jahar Neja
Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai farmaki yankin jihar Neja, sun sace Rabaran da wasu mutane sama da 40.
Wannan na zuwa jim kadan bayan da gwamnati ta karfafi gwiwar mazauna kan komawa yankunansu.
Rahotanni sun tattaro cewa, kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin.
jihar Neja – Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki Neja jiya Lahadi sun yi awon gaba da limamin cocin Katolika na Cocin St Mary da ke Sarkin Pawa, hedikwatar karamar hukumar Munya ta Jihar Neja, Rabaran Leo Raphael Ozigi da wasu mutanen kauyen 44.
Daily Trust ta ce ta samu labarin cewa, an yi garkuwa da Rabaran ne a hanyarsa ta zuwa Gwada daga Sarkin Pawa a lokacin da ya ci karo da ‘yan bindiga da ke barna, inda suka yi taho-mu-gama da shi tare da wasu mutanen kauyen.
Sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Neja, Fasto Raphael Opawoye, ya tabbatar da sace Rabaran Ozigi.
A cewarsa:
Read Also:
“An yi garkuwa da Rabaran Dr Leo Raphael Ozigi ranar Lahadi a hanyarsa ta komawa Gwada daga Sarkin Pawa bayan hidimar bautar ta ranar Lahadi.”
Sakataren karamar hukumar Munya, James Jagaba, ya bayyana sabon barnar ‘yan bindiga a karamar hukumar Munya a matsayin abin takaici.
Yace:
“Ilahirin hukumar Munya tana cikin tashin hankali. Halin da ake ciki a yankin yana da ban tsoro. Ana yin garkuwa da mutane a dukkan sassan kananan hukumomin.”
An sace wasu mutane 44 a yankin
Wani mazaunin yankin mai suna Shehu Abubakar, ya shaida wa Daily Trust cewa wasu mutanen kauyen 44 da aka sace na daga cikin wadanda suke koma yankunansu daga sansanonin ‘yan gudun hijira a ranar Asabar.
A cewarsa:
“Muna cikin damuwa saboda da alama matsalar mu ba ta kare ba. Jama’a sun fara dawowa ranar Asabar don shirin noman doya.
“Gwamnati ta karfafe mu mu koma ga yankunanmu cewa za a yi shirye-shiryen magance tsaro. A ranar Asabar ne mutane suka fara dawowa kuma wadannan miyagu sun sake farmakarmu.”
Abubakar ya koka da yadda ‘yan bindigan da ke cin karensu ba babbaka tun ranar Asabar suke barna a hanyar Sarkin Pawa zuwa Gwada tare da garken shanun da suka yi awon gaba da su a lokacin da suke kai hare-hare kan mazauna.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 17 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 11 hours 58 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com