Yanayin Tsaro: Kamfanin Jirgin Saman Azman ya Dakatar da Zirga-Zirga a Kaduna
Kamfanin jirgin saman Azman ya dakatar da zirga-zirga a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya kwanaki kadan bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai filin jirgin saman jihar inda suka kashe masu gadi da wasu ma’aikata
Read Also:
Kamfanin ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa zai dakatar da zirga-zirga a Kaduna daga ranar Litinin din da ta wuce.
Kamfanin ya ce ya dauki matakin saboda yanayi na tsaro a filin jirgin saman.
Matakin kamfanin dai ya sa matafiya sun yi cirko-cirko a filin jirgin saman na Kaduna saboda karancin jiragen da za su kai su inda za su je.
Hukumar gudanarwar kamfanin ta sanar da cewa za a dakatar da zirga-zirgar ce zuwa wani lokaci ma’ana kafin yanayin tsaro ya inganta a filin jirgin saman na Kaduna.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 14 hours 38 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 16 hours 20 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com