Yajin Aikin ASUU: Za mu Mayar da Titunan Abuja Ajujuwanmu Har Zuwa Lokacin da aka Bude Makarantu – NANS
Daliban Najeriya karkashin kungiyar NANS za su cigaba da yin zanga-zanga a titunan Abuja kan yajin aikin da ASUU ke yi.
Sunday Asefon, shugaban kungiyar daliban, NANS, ya ce ba za su dena zanga-zangar ba har sai an bude dukkan jami’o’in da ke kasar.
A cewarsa, tunda an rufe ajujuwansu na makaranta, za su mayar da titunan Abuja ajujuwansu har zuwa lokacin da aka bude makarantun.
FCT, Abuja – Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, a ranar Litinin ta cigaba da zanga-zangar ta na neman ganin an kawo karshen yakin aikin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ke yi.
Read Also:
Da ya ke magana a yayin zanga-zangar a Abuja, shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya ce daliban a shirye suke su fito su mamaye manyan titunan Abuja, rahoton The Punch.
Mun gaji, ba mu damu da abin da zai faru ba sakamakon zanga-zangar, Shugaban NANS
Ya kara da cewa daliban sun gaji kuma ba za su fasa abin da suka fara ba har zai an bude dukkan jami’o’i a kasar.
Asefon ya ce:
“Tunda sun kore mu daga ajujuwan mu za mu mayar da titunan Abuja dakunan karatun mu.
“Wannan ba wasan yara bane, da gaske muke yi a yanzu. Sakon mu mai sauki ne: A bude mana jami’o’in mu. Mun tabbatar idan ba a janye yakin aikin nan ba, Daliban Najeriya ba za su bar tituna ba.
“Za mu koma titunan ba tare da damuwa da abin da zai faru ba. Mutanen Abuja su sani cewa za mu mamaye manyan titunan a matsayin wani mataki na ganin an bude makarantun mu.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 46 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 27 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com