‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Birnin Tarayya Abuja
Wani rahoto ya bayyana yadda ‘Yan bindiga suka yiwa karamar hukumar Mulki ta Gwagwalada dake Birnin Tarayya Abuja tsinke, inda suka hallaka Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyetti Allah (MACBAN) Adamu Aliyu.
Maharan sun halaka Aliyu ne da wasu Karin mutum 4 a daura da kauyen Daku dake mazabar a ranar Alhamis.
Sakatararen Kungiyar ta MACBAN Muhammad Usman, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar lahadi, yace an yi garkuwa da mutum 3, bayan da wasu mutum suka sami raunukan harbi a jikin su inda suke karbar kulawa a Asibitin Koyarwa na Gwagwalada.
Yace lamarin ya auku ne a ranar Alhamis, da misalin karfe 5 na yamma, yayin da Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah ke kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Izom dake jihar Niger a cikin wata motar daukar kaya, nan ne ‘Yan bindigar suka fito daga cikin daji suka kuma bude wuta kan motar.
Yace ‘Yan bindigar sun fasa gilashin motar da shugaban kungiyar ta MACBAN da wasu fasinjoji ke ciki.
Read Also:
“Suna kan hanyar su ta dawowa daga sayar da shanu a kasuwar Izom ta jihar Niger, kilomita 1 ne rak ya rage musu su karaso kauyen Daku, nan ‘Yan bindigar suka afka musu da harbi daga daji, nan suka hallaka Shugaban Kungiyar ta MACBAN tare da wasu mutum 4” a cewar sa.
Ya kuma bayyana sunayen wadanda aka hallakar da suka hadar da Saleh, Aliyu, Muhammadu da kuma Saidu, yace tuni aka yi musu sutura kamar yadda addinin muslunci yayi tanadi.
Sai dai jaridar Daily trust ta rawaito cewa jami’an tsaro da suka hadar da Jami’an Civil Defence, ‘Yan Sanda Kwantar da Tarzoma ‘Yan Sa Kai ne suka halarci jana’izar.
Shugaban Karamar Hukumar Mulki ta Gwagwalada Alhaji Adamu Mustapha, ya tabbatarwa da wakilin mu faruwar lamarin ta wayar tarho, amma yace zai masa Karin bayani bayan ya kammala wata ganawar sirri da yake tsaka dayi a lokacin.
Duk kokarin da mukayi domin jin ta bakin kakakin rundunar ‘Yan Sandan birnin tarayya Abuja DSP Adeh Josephine, bata amsa kiran wayar ba, kuma bata biyo sakon karta kwanan da muka tura mata ba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 19 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com