• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Taska Yadda Shugaban NITDA ya Sanya Farin Ciki a Zukatan Marayu a Jahar...
  • Taska

Yadda Shugaban NITDA ya Sanya Farin Ciki a Zukatan Marayu a Jahar Jigawa

By
Prnigeria
-
April 14, 2022
Arewa Award

Yadda Shugaban NITDA ya Sanya Farin Ciki a Zukatan Marayu a Jahar Jigawa

 

Yara marayu na daga cikin rukunin mutane waɗanda bakasafai al’umma ke damuwa da duba da halin da su ke ciki ba, balle har su kai ga tunanin ware wasu maƙudan kuɗaɗe wajen tallafawa rayuwarsu ba, sai dai kuma mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) ya sha bamban da saura domin kuwa ya kasance jami’in gwamnatin tarayya na farko ɗan asalin Jihar Jigawa wanda ya tuna da marayu a duk kafatanin ƙananan hukumomin Jihar guda (27) ya tallafa musu.

Kimanin buhun shinkafa (2700) Malam Kashif Inuwa Abdullahi ya ba wa kwamitin marayu na ƙungiyar Izala aka rabawa marayun a ƙarƙashin gidauniyarsa ta aikin alkhairi gami da tunawa da mahaifinsa, (Malam Inuwa Foundation).

A cikin jimillar buhun shinkafar guda (2700), kowacce ƙaramar hukuma ta samu jimillar buhu (100) ga gidajen marayu ɗari, wanda kuma aka rabar a ranar 5 ga watan Afrelu, zuwa 12 ga watan na Afrelu, 2022. Kwamitin marayu na ƙungiyar ta Izala su ne su ka haɗa sunayen marayun a kowacce ƙaramar hukuma birni da kewaye su ka zaɓo waɗanda su ka fi buƙata aka kuma ba su wannan tallafi batare da wani bambanci ko sanayyar alfarma ba, (cancanta zalla aka bi wajen zaɓo waɗanda aka ba wa).

Bayyana irin wannan aikin alheri wanda babu manufar tozarta waɗanda su ka amfana, kana kuma babu manufar riya cikinsa, ya na taimakawa ne wajen zaburar da sauran al’umma musamman mawadata wajen cigaba da samar da tsare-tsaren tallafawa yara marayu da sauran mutane masu rauni, gami da fitar da shakku da munanan zarge-zargen: (“ba a taimakawa” a zukatan jama’a kan shugabanni) wanda kuma addini bai ƙyamaci bayyana duk wani nau’in alkhairi da kykkyawar manufa ba.

Mutanen da su ka amfana, da ma sauran al’umma daban-daban, sun bayyana farin ciki matuƙa da godiyarsu bisa wannan abin alheri. Misali: Amina Shu’aibu, yarinya ce marainiya ƴar asalin ƙaramar hukumar Buji, ga abin da ta ce jim kaɗan bayan an ba ta tata shinkafar “Ni marainiya ce, babana da iyata duk sun mutu, yayana ne ya ke riƙe da ni, ina godiya da samun wannan tallafi Allah Ya saka da alkhairi”. Inji ta.

Shi ma wani dattijo wanda ya amfana mai suna Ali na Ali ɗan asalin ƙaramar hukumar Kiyawa, ya bayyana godiya da farin cikinsa gami da addu’a kamar yadda ya ce: “mun gode, Allah Ya yalwata dukiyar Malam Kashif Inuwa, Allah Ya saka masa da alkhairansa, Allah Ya kai ladan kabarin magabata”. Inji shi ya yin da aka ba shi.

Read Also:

  • Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu – OPEC
  • Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyya
  • A aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a Mangu

A ɗaya gefen kuma, su ma shugabannin kwamitin marayun na kowacce ƙaramar hukuma sun bayyana godiya da farin cikinsu kamar haka: “wannan tallafi abu ne mai muhimmanci musamman duba da yadda ake fama da tsadar rayuwa, duk waɗanda aka tallafawa ba shakka sun ji daɗi, mu na fatan Allah Ya saka masa da alkhairi Ya kuma sanya sauran masu hali su yi koyi da shi”. Inji Malam Auwal Shu’aibu Musa Yayarin Tukur, shugaban ƙungiyar Izala na ƙaramar hukumar ta Buji.

Haka zalika, “mu na roƙon Allah yadda Malam Kashif Inuwa Ya kula da marayu Allah Ya kula da shi, Allah Ya sa randa zai bar duniya Ya bar nasa marayun shi ma Allah Ya kula masa da su, mun yi farin ciki matuƙa Allah Ya ji ƙan Malam Inuwa”. Cewar Malam Ibrahim Chiroma Birnin Kudu, ɗaya daga cikin shugabannin kwamitin marayu na ƙaramar hukumar Gumel.

Shi ma a nasa tsokacin, Malam Umar Usaini Jahun, shugaban kwamitin marayu na ƙungiyar Izala na Jahun, ya bayyana cewa: “mu na godiya marar iyaka ga Malam Kashif Inuwa bisa wannan taimako da ya yi, wannan ba wai abu ne farau na taimako da ya ke yi ba domin ni shaida ne banda wannan akwai abubuwa da dama na taimako da ya yi, mu na godiya sosai Allah Ya sa masa a mizani, Allahi Ya taimake shi kamar yadda ya ke taimakon addinin Islam”.

Su ma iyayen ƙasa, hakimai waɗanda rabon tallafin shinkafar ya gudana a kan idonsu, sun bayyana nasu farin cikin da godiya gami da fatan alkhairi, misali: “Babban fatana Allah Ya saka masa da alkhairi, Allah sa Ya gama lafiya, Allah Ya kai ladan ga dukkan magabata da su ka rasu, Allah Ya tsare dukkan abin ƙi, Allah Ya ƙara arziƙi, Allah Ya sa mutane dayawa su yi koyi da shi”. Inji mai girma sarkin ban Ringim, Hakimin Ɓaɓura, Alhaji Nata’ala Mustapha.

Shi ma a nasa jawabin, mai girma Hakimin Miga, Alhaji Sani Yakubu, ya bayyana cewa: “Wannan kusan shi ne karon farko da wani mutum wanda ba ɗan yankinmu ba ya kawo mana wannan abin alkhairi domin marayu da masu ƙaramin ƙarfi, mun gode Allah Ya saka”.

Haka zalika, “Ya kamata sauran mawadata su yi koyi, duk wanda ya ke da hali ya kamata ace ya na da irin wannan gidauniya ta Malam Kashif Inuwa saboda anan Arewa ne za ka ga almajirai wanda da ace da irin wannan gidauniya to da duk haka ba ta kasance ba, da an samu sauƙin matsalolin, mu na fatan sauran mawadata za su yi koyi, mun gode Allah Ya saka da alkhairi”. Cewar mai girma Sarkin Dawakin Gumel, hakimin Maigatari, Alhaji Sani Alhassan wanda Malam Yakubu Aminu ya wakilta wajen rabon.

Kafatanin marayun da su ka samu tallafin za su yi amfani da shinkafar ne tare da sauran ƴan gidansu, wanda ɗumbin jama’a ne su ke kwana babu abin da za su ci, wanda hakan kuma ya sanya mutane da dama godiya da addu’a gami da jinjinar fatan alkhairi ga Malam Kashif Inuwa bisa wannan tallafi ga marayun a daidai gaɓar da wasu masu iyaye rayen ma buƙata su ke tare da zaburar da sauran masu hali da su yi koyi domin jinƙai da agaji ga rayuwar marayu.

Garba Tela Haɗejia

Laraba, 12 ga watan Ramadan, 1443.

Laraba, 13 ga watan Afrelu, 2022.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 9 hours 14 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 10 hours 55 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • Jigawa
  • Malam Inuwa Foundation
  • Malam Kashifu Inuwa Abdullahi
  • Marayu
  • NITDA
Previous articleYanzu – Yanzu: Dattawan Arewa Sun Bukaci Buhari yayi Murabus
Next articleTSARO: Dakarun Sojin Hadin Gwuiwa na MNJTF Sun Hallaka Mayakan Kungiyar ISWAP.
Prnigeria

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP

Magance Karancin Naira: CBN ya Umarci Bankuna da su yi Aiki a Ranakun Asabar da Lahadi

Hatsarin Mota ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 25 a Bauchi

Hukumar NITDA ta Gabatar da Satifiket ga Matan da Suka Samu Horo Kan Fasahar Zamani

Ambaliyar Ruwa a Jigawa: Gidauniyar Ƙasar Qatar da ta Malam Inuwa Sun Raba Tallafin Abinci ga Mutane 1,000

An Gudanar Da Bikin Arewa Stars 30 Under 30 2022, Cikin Nasara

Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago

‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Kashe ‘Yan Sanda Biyu a Anambra

Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

Gidauniyar Malam Inuwa ta Ɗauki Nauyin Koyar da Ƴa’yan Fulani Al-ƙur’ani

Bincike: Shin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ƙirƙiro da Tambayoyi Domin Tantance kungiyoyin Musulmi da Kirista a kidayar 2023? 

Recent Posts

  • Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu – OPEC
  • Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyya
  • A aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a Mangu
  • Najeriya na fuskantar tsaiko kan shirinta na karɓar Dala biliyan 5 daga Saudiya
  • Bom ya kashe masu yawon murnar sallah a Sakkwato

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 9 hours 14 minutes 30 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1444 days 10 hours 55 minutes 55 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu - OPECTinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi kan ranar dimokuraɗiyyaA aƙalla mutum 20 sun rasa rayukansu a saboda hare-hare a ManguNajeriya na fuskantar tsaiko kan shirinta na karɓar Dala biliyan 5 daga SaudiyaBom ya kashe masu yawon murnar sallah a SakkwatoNan bada jimawa ba za a samu sauyi a ɓangaren man fetur na Najeriya - DangoteSojojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 10 a ZamfaraAn samu tashin gobara a masaukin alhazan Najeriya a Shari MansurGwamnatin Neja na yunƙurin haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man feturJirgin sojoji ya kashe ƴan sa-kai a ƙoƙarin fatattakar ƴanbindiga'Hadarin mota ya yi sanadiyyar matasa 22 'yan asalin KanoGwamnatin Tinubu ta jefa ƴan Najeriya fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci - NLCSojoji sun ce sun hallaka ƴan ta'adda 60 a jihar BornoAn kama mutane 41 kan zargin kashe DPO a KanoRayuwar ƴan Najeriya na ƙara inganta - Tinubu
X whatsapp