Hukumar kula da gasar firimiya ta Najeriya, Nigeria Professional Football League (NPFL), ta bai wa ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars damar ci gaba da buga wasanni a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano.
Wannan dai na cikin Wata sanarwa da hukumar ta aike wa kungiyar ta kano Pillars, inda ta ce yanzu haka kungiyar nada damar buga wasannin a filin bayan duba na tsanaki da hukumar tayi.
Read Also:
Ta cikin sanarwar Hukumar ta ce wajibi ne kungiyar ta kano Pillars ta tanadi wani filin wasan da za ta ci gaba da buga wasanni da zarar an fara aikin gyara ciyawar filin taka leda ta filin kafin kammala shi.
Tuni kungiyar kwallon kafar ta kano Pillars ta amince da sharaɗin, har, inda tace za ta buga wasanta na gaba tare da kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a Kano ranar 16 ga watan Afrilu.
Idan dai za’a iya tunawa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ba ta buga wasa a gida ba a kakar bana sakamakon matakin da hukumar ta NPFL ta ɗauka, inda ta umarci a sauya ciyawar filin taka ledar.
Yanzu haka dai kungiyar ta Pillars na mataki na 13 da maki 26 bayan buga wasa 22 a kakar bana ta 2022/2023.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 43 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 24 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com