Home Taska Gidauniyar Malam Inuwa ta Rabawa Marayu 100 Tallafin Turmin Atamfa 

Gidauniyar Malam Inuwa ta Rabawa Marayu 100 Tallafin Turmin Atamfa 

Tallafin Marayu

Gidauniyar Malam Inuwa ta Rabawa Marayu 100 Tallafin Turmin Atamfa 

 

A ƙoƙarin da ta ke kan cigaba da yi wajen ganin ta kyautatawa marayu a Jihar Jigawa a wannan wata na Ramadan mai albarka, Gidauniyar Malam Inuwa wacce mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE) ya assasa, ta rabawa marayu mata (100) tallafin turmin Atamfa domin hidimar sallah a ƙaramar hukumar Haɗejia da ke Jihar Jigawa.

Rabon wanda aka gudanar a yammacin wannan rana, a ofishin gidauniyar da ke kan titin Garun-Gabas, Haɗejia, ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shugabannin gidauniyar, da kwamitin marayu na ƙaramar hukumar waɗanda su ka zaƙulo marayun da su ka fi buƙatar temako a mazaɓun yankin gabaɗaya.

Marayun da su ka halarci wurin rabon su ka karɓa, da kuma wakilan marayun waɗanda su ka karɓa musu, gabaɗaya sun bayyana godiya da farin cikinsu tare da addu’ar fatan alkhairi ga mai girma shugaban hukumar ta (NITDA), Malam Kashif gami da fatan Allah Ya ji ƙan mahaifin nasa, Malam Inuwa Ya ƙara arziƙi.

Talata, 19 ga watan Afrelu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp