Mahaifina ne ya Ɗora ni Akan Cewa Duk Abin da na Samu ba Nawa ne ni Kaɗai ba – Shugaban NITDA, Malam Kashifu Inuwa
A wani mataki da ke nuni da irin tarbiyyar da mahaifinsa ya ɗora shi a kai tun a lokacin da ya ke kan tasowa gabanin rasuwarsa, mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya bayyana cewa ayyukan da gidauniyarsa ta ke gudanarwa su na faruwa ne saboda irin tarbiyya tagari da mahaifinsa ya yi.
Malam Kashif Inuwa Abdullahi, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni, 2022 a garin Haɗejia, jim kaɗan bayan sun kammala rabon kayan tallafin sana’o’i da gidauniyar ƙasar Qatar da haɗin gwiwar tasa gidauniyar su ka samarwa al’umma a Jigawa.
Tunda farko, Malam Kashif Inuwa, ya fara ne da bayyana cewa: “Ita wannan gidauniya mun fara ta ne a saboda abin da mahaifinmu ya ɗora mu a kai tun a lokacin da mu ke tasowa cewa: duk abin da ka samu ba naka ne na kai kaɗai ba, naka ne na kai da ƴan uwanka. Tun a lokacin ko irin an aike ka an ba ka wani abu, ko ka zo da wani abu, zai ce ka raba ka ba wa ƴan wanka”. Inji Malam Kashif Inuwa Abdullahi.
Daga nan ya cigaba da cewa: “A lokacin da na fara karɓan tallafin karatu (Schoolarship) shi ne ya sa ni na rabar da kuɗin nan gabaɗaya ga ƴan uwa, a lokacin har zuciyata ma na cewa mai ya sa zai sa na yi haka ni ma da zan koma makaranta, amma saboda bin umarni dole na rabar da kuɗin duka. Lokacin da zan koma makaranta ya ɗauko kuɗi daga aljihunsa ya ba ni. Tun lokacin duk lokacin da na karɓi kuɗin tallafin karatu (Schoolarship) zai sa na raba shi gida (4) ya ce na raba kashi (1), kashi (3) cikin (4) kuma na ɗauka na yi amfani kaina da shi”.
Malam Kashif Inuwa, ya kuma ƙara da cewa: “Ko lokacin da na fara ɗaukan albashi da na fara aiki, albashin farko haka shi ma ya sa duka na rabar, na biyun ya sa na raba kashi huɗu na rabar kashi ɗaya kashi uku kuma na ɗauka na yi amfani da shi. To tun lokacin abin da na ke yi kenan har yau. Da na ga abin kuma ya na bunƙasa masu buƙatar kuma su na da yawa kuma Allah Ya hore za ka ga mutum ba wai iya ƴan’uwanka ne kawai ba, akwai maƙota, akwai abokai da sauransu, da haka sai mu ka fara taimakawa abokai da ƴan’unguwa da sauransu,”. Cewar Malam Kashif Inuwa.
Daga nan kuma sai ya cigaba da cewa: “Sai na ga domin a samu ɗorewar abin zai fi kyau a samu wata gidauniya saboda idan yau ina da hali gobe ba dole ne ya zama ina da hali ba, amma su waɗanda ka saba taimakawa wani idan ba ka nan shi kuma ƙarshen jin daɗinsa kenan, amma in aka samu irin gidauniyar nan sai a samu ƴan’uwa da abokan arziƙi su riƙa taimakawa, haka mu ka fara abubuwan mu ke abubuwan da zai taimakawa mutane da wanda zai kawo cigaba a gari”. Cewar Malam Kashif.
Read Also:
Dangane da batun alaƙar gidauniyar tasa da ƙungiyoyin ba da agaji na Duniya kuwa, Malam Kashif Inuwa ya yi bayanin cewa: “kuma sai mu ka ga ashe ma za mu iya zuwa mu yi haɗin gwiwa da wasu gidauniyar musamman ita wannan gidauniya ta ƙasar Qatar da kuma ta matasa musulmai ta Duniya, (WAMY). Mu na da kykkyawar fahimta da su, mu na da haɗin gwiwa da su, duk wani aiki da za su yi a Nageriya mu na cikin waɗanda su ke shawara da su, su ga a ina ya dace a yi, mai ya kamata a yi, shi ya sa mu ka ga indai an yi shawara in bai fi ƙarfinmu ba, za mu ce a kawo gida saboda komai an ce ka fara daga inda ka fito, shi ya sa za ka ga mu na kawo su,”. Iniji Malam Kashif”.
Da ya ke tsokaci dangane da nasarorin da aka samu daga lokacin da su ka ƙulla alaƙar haɗin gwiwar da ƙungiyoyin ba da agajin na Duniya zuwa yau, Malam Kashif Inuwa ya bayyana cewa: “Daga lokacin da mu ka fara da su zuwa yanzu, akwai masallatai waɗanda aka kammala da waɗanda ake kan aikinsu kimanin guda ɗari uku da hamsin a cikin Jihar nan (Jigawa), akwai rijiyoyin ruwa masu amfani da hasken rana guda ɗari biyu da tamanin da su ka yi”.
Da ya juya kan batun shirinsu na rabon kayan tallafin sana’a kuwa, Malam Kashif Inuwa ya bayyana cewa: “Dan haka yanzu sai su ka ce ai za su iya ma wasu abubuwan, shi ne mu ka fara wannan harka ta baiwa mutane abin da za su yi sana’a. Kamar yau an rabawa mutane wajen ɗari uku da hamsin kayayyakin sana’a daban-daban, akwai waɗanda aka ba su keken ɗinki, akwai waɗanda aka ba su mashin, akwai waɗanda aka ba su injin niƙa, akwai waɗanda aka ba su na’ura mai ƙwaƙwalwa”. -Inji shi.
Da ya juya kan batun shirinsu na gina gidaje kuwa, Malam Kashif Inuwa ya yi tsokaci kamar haka: “Bayan haka kuma, sai su ka ce ai akwai waɗanda ma ba su da gida, ba za su iya gidansu na kansu ba a rayuwa, shi ya sa su ka ce za su zo su gina gidaje guda hamsin da makaranta da masallaci waɗanda su ma za a ba wa mabuƙata, (mutanen da ba za su iya gina gida ba), a ba su wannan gidajen don su samu sauƙin rayuwarsu”. Cewar Malam Kashif Inuwa.
Daɗi da ƙari kuma, ya cigaba da cewa: “Duka abubuwan da mu ke yi ba wai abubuwa ne da kuɗi ya ke fitowa daga aljihunmu ba, yawanci mutanen da aka sani ne su ke taimakawa da kuma irinsu gidauniyar ta ƙasar Qatar”. Inji shi.
Malam Kashif Inuwa ya kuma ƙarƙare da nanata cewa: “Kamar yadda na faɗa tunda farko, wannan abu ne da na taso mahaifinmu ya ɗora ni a kai, duk sanda na yi ina jin daɗi. Na farko na yi abin da mahaifina ya ce na yi, na biyu kamar na sauke wani nauyi ne a kaina saboda shi Allah ma ya ce idan ya ba ka ba wai kai kaɗai ya ba wa ba, har ƴan’uwanka da abokan arziƙi. Ba abin da ya fi faranta min rai irin na ga wani mutum mai damuwa ya zo irin damuwarsa ta kai damuwa in taimaka ya samu wani sauƙi,”. Cewar mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa A. (CCIE).
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 5 hours 58 minutes 26 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 7 hours 39 minutes 51 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com