Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Litinin, ta ci tarar malamin addinin Musulunci da ake tsare, Malam Abduljabbar Nasiru Kabara, Naira Miliyan 10 bisa shigar da kara kan tabbatar da hakkinsa na ɗan ƙasa, inda kotun ta ce hakan rashin ɗa’a ne ga kotun.
Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a biya wadanda ake kara kudaden; da su ka haɗa da Kotun Shari’a ta Kofa Kudu, Kano, da gwamnatin jihar Kano a matsayin waɗanda a ke kara na daya da na biyu.
Read Also:
Mai shari’a Nwite ya kuma baiwa Kabara da lauyansa Shehu Dalhatu umarnin su biya gwamnatin jihar Naira dubu Dari.
Alƙalin kotun ya ce da zarar kotu ta gamsu cewa an saɓawa tsare-tsaren kotu wajen shigar da ƙara, to kotu na da hakkin hukunta wanda ya shigar da karar.
Ya ce matakin da lauyan Kabara ya dauka na da nufin samun hukuncin da ya dace ko ta halin kaka.
Nwite ya ce shigar da kara a cikin wata kara mai lamba: FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma zuwa Abuja don shigar da ita dai wannan ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1201/2022 kan wannan batu da lauyan ya yi abin Alla-wadai ne.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 59 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 40 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com