Home General Gwamnatin Nijeriya Zata Ciyo Bashin Tiriliyan 12 Domin Cike Gibin Kasafin Shekarar...

Gwamnatin Nijeriya Zata Ciyo Bashin Tiriliyan 12 Domin Cike Gibin Kasafin Shekarar 2023

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗi na 2023 da ya kai naira tiriliyan 19.76 a gaban gamayyar majalisun dokokin Nijeriya a  ranar Juma’a.

Kasafin shi ne na ƙarshe da shugaban ya gabatar yayin da yake shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Buhari yace yana son ya bar abin tarihi a kasar fiye da yadda ya same ta a 2015.

Wannan ne kasafin kuɗi mafi yawa a tarihin Najeriya, inda ya zarta na shekarar 2022 da kashi 15.37 – wanda aka gabatar kan naira tiriliyan 17.13.

Kasafin kuɗin yana da giɓin da sai gwamnati ta hada da rance za ta cike fiye da rabin sa, wanda ya kai tiriliyan 12.

Gwamnatin tarayyar Nijeriyar ta bakin Ministar Kuɗi Zainab Shamsuna ta ce za ta cike giɓin ne ta hanyar ciyo bashi da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnati.

Kazalika akwai batun tallafin man fetur, wanda shi ma ƙarin dawainiya ne ga kasafin, wanda zai iya janyo zazzafar muhawara, kasancewar wasu na goyon bayan gwamnati ta ci gaba da ba da shi, yayin da wasu ke ganin ya kamata a dakatar, saboda a nasu ra’ayin masu hada-hadar man sun fi talaka cin gajiyar tallafin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp