Home General Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya tayi Martani ga kasashen Ketare

Rundunar ‘Yan sandan Nijeriya tayi Martani ga kasashen Ketare

Bayan Birtaniya da Australia sun bukaci ‘yan kasarsu su guji zuwa Najeriya saboda dalilai na tsaro.

rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce kasar na cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya har zuwa lokacin zabe, inda ta kara da cewa ba wannan ne karon farko da kasashen ketare ke fitar da sanarwar mai kama da wannan ba ga ‘yan kasarsu.

Tun da fari dai a cikin wani sakon shawarwari kan tafiye-tafiye, gwamnatin Australia ta bukaci janye duk wani shiri ko tunanin zuwa Najeriya ga ‘yan kasarta saboda ana shirin gudanar da manyan zabuka a kasar, kuma akwai fargabar da ake ta barkewar tashe-tashen hankula da ke da nasaba da zabe.

Cikin sakon, gwamantin ta Australia ta ce akwai zargin hare haren da ake kitsawa na kai hari kan ofisoshin hukumar zabe, don haka kasar ta shawarci ‘yan kasarta da su nisanta kansu da zuwa Najeriya.

Itama gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin cewa za a iya samun barkewar zanga-zanga a lokacin zabe, don haka ne ta shawarci ‘yan kasarta da zaune a Najeriyar da ma wadanda ke shirin zuwa kasar da su guji zuwa Najeriya musamman a wannan lokaci da zabuka ke tafe a Najeriya.

Kazalika itama kungiyar Tarayyar Turai, ta yi gargadin cewa rashin tsaro na iya hana a gudanar da zabe a wasu sassan kasar ta Najeriya.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai kasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Jamus da Bulgeriya suka fitar da sanarwar kan ta’addanci, inda suka gargadi ‘yan kasarsu a Najeriya da su guji manyan shagunan siyar da kayayyaki da wuraren ibada da otal-otal da suka ce ‘yan ta’adda za su iya kai wa hari.

Sai dai Gwamnatin Tarayyar kasar ta yi watsi da wannan gargadi, inda ta bayyana su a matsayin na karya, ta kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da harkokinsu bisa doka domin kasar na cikin kwanciyar hankali.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp