• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Taska Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP
  • Taska

Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP

By
Prnigeria
-
March 25, 2023
Court
Arewa Award

Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP

 

Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon ƙasa EFCC ta sake gurfanar da Mamman Ali, ɗa ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasar Ahmadu Ali, bisa zargin zambar naira biliyan 2.2 na tallafin man fetur.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, ya ruwaito cewa an sake gurfanar da Mamman Ali tare da wani mutum mai suna Christian Taylor da kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd. a gaban wata kotu a birnin Legas.

An gurfanar da su ne bisa zarge-zagen laifuka 49 ciki har da haɗa baki, da yaudara da zamba cikin aminci, da yin ƙarya domin karɓar kuɗi da amfani da takardun bogi.

To sai dai mutanen sun musanta duka zarge-zargen da ake yi musu.

Lauyan hukumar EFCC Samuel Atteh, ya nemi kotun da ta sanya ranar sauraron ƙarar ta yadda zai gabatar da shaidunsa da za su tabbatar da zargin da hukumar ke yi wa mutanen.

Read Also:

  • Nan gaba za ku ga Amfanin dokar haraji -Tinubu
  • Amurka ta fara kai harin soji Arewacin Nijeriya
  • Sojoji sun daƙile yunƙurin harin ƴanbidiga a Borno

To sai dai lauyan waɗanda ake zargin Kolade Obafemi ya nemi kotun da ta bayar da belin waɗanda yake karewa.

To amma lauyan EFCC ya ce abu mafi muhimmaci kan wannan shari’a shi ne waɗanda ake zargi su riƙa halartar kotun don fuskantar tuhumar da ake yi musu.

Daga ƙarshe alƙalin kotun ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake zargin su ci gaba da kasancewa a hannaun hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a gabatar da takardun neman belinsu a hukumance.

Alƙalin ya kuma ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu mai zuwa.

A ɗaya daga cikin zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi wa mutanen, shi ne zargin haɗa baki don karɓar naira miliyan 750 daga gwamnatin tarayya, don karyar bai wa kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd, ƙarƙashin asusun tallafa wa kamfanonin mai don shigo da litar mai 10,031,986, da kamfanin na Nasaman Oil Services Ltd, ya yi iƙirarin cewa ya saya daga kamfanin man Birtaniya na SEATAC Petroleum Ltd.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
  • TAGS
  • efcc
  • PDP
Previous articleMagance Karancin Naira: CBN ya Umarci Bankuna da su yi Aiki a Ranakun Asabar da Lahadi
Next articleAdamawa: Ayyana Zaɓen Gwamna a Matsayin Wanda bai Kammala ba shi ne Daidai – Binani
Prnigeria

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Azumin Bara: Talge Muka Riƙa Sha a Hannun Maharan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Magance Karancin Naira: CBN ya Umarci Bankuna da su yi Aiki a Ranakun Asabar da Lahadi

Hatsarin Mota ya yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 25 a Bauchi

Hukumar NITDA ta Gabatar da Satifiket ga Matan da Suka Samu Horo Kan Fasahar Zamani

Ambaliyar Ruwa a Jigawa: Gidauniyar Ƙasar Qatar da ta Malam Inuwa Sun Raba Tallafin Abinci ga Mutane 1,000

An Gudanar Da Bikin Arewa Stars 30 Under 30 2022, Cikin Nasara

Manomi Yayiwa Wata Mata Yankan Rago

‘Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi da Kashe ‘Yan Sanda Biyu a Anambra

Gidauniyar Malam Inuwa Da Kokarinta Na Ilmantar Da Mutanen Karkara Da Rugage

Gidauniyar Malam Inuwa ta Ɗauki Nauyin Koyar da Ƴa’yan Fulani Al-ƙur’ani

Bincike: Shin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta ƙirƙiro da Tambayoyi Domin Tantance kungiyoyin Musulmi da Kirista a kidayar 2023? 

An Cire Mukaddashin Babban Akantan Najeriya, Mr Chukwuyere Anamekwe

Recent Posts

  • Nan gaba za ku ga Amfanin dokar haraji -Tinubu
  • Amurka ta fara kai harin soji Arewacin Nijeriya
  • Sojoji sun daƙile yunƙurin harin ƴanbidiga a Borno
  • Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da kudirin hukuncin kisa ga masu garkuwa
  • ADC ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1660 days 15 hours 54 minutes 35 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1642 days 17 hours 36 minutes 0 second

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Nan gaba za ku ga Amfanin dokar haraji -TinubuAmurka ta fara kai harin soji Arewacin NijeriyaSojoji sun daƙile yunƙurin harin ƴanbidiga a BornoGwamnatin Nijeriya ta yi watsi da kudirin hukuncin kisa ga masu garkuwaADC ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar harajiGwamnati Nijeriya ta haramta fitar da itace zuwa ƙasashen wajeTinubu ya maye gurbin Engr Farouk daga shugabancin hukumar NMDPRAICPC ta ce zata binciki shugaban hukumar NMDPRAZa mu ci gaba da kamen masu bakin gilashin mota - Yan sandaMajalisa ta amince da naɗin sabbin jakadun da Tinubu ya gabatarShugaban Najeriya zai iya dakatar da gwamna - Kotun ƘoliGwamnan Kano Ya Kafa Runduna ta Musamman Don Tabbatar da Tsaro a Tashoshin MotaNNPC ya fara bincike kan fashewar bututun mai a jihar DeltaKotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam SandaKotu ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige gidan yari
X whatsapp