‘Yan Afrika miliyan 1 na rayuwa da tarin fuka ba tare da sani ba- WHO

A jawabinta yayin bikin ranar yaki da cutar ta tarin fuka ko kuma TB, Shugabar hukumar ta WHO reshen Afrika Dr Matshidiso Moeti ta ce cutar na ci gaba da kisan mummuke ga miliyoyin al’ummar Afrika inda yanzu haka ake da jumullar mutanen da yawansu ya haura miliyan 1 da ke dauke da cutar amma ba tare da sani ba.

A cewar Moeti duk da kokarin da hukumar ta WHO ke yi da taimakon kungiyoyi masu zaman kansu da ke aikin yaki da cutar ta hanyar wayar da kai da kuma bayar da magunguna har yanzu akwai wakeken gibi a kokarin kawar da cutar tsakanin al’ummar nahiyar.

Shugabar ta WHO shiyyar Afrika ta ce lura da tazarar da ke tsakanin alkaluman wadanda suka yi rijistar cutar da kuma wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar hakan na nuna yawan mutanen da ake da su wadanda basu san suna dauke da cutar ta TB ko kuma tarin fuka ba.

Dr Matshidiso Moeti ta ce kasha 40 cikin 100 na masu dauke da cutar TB a Afrika ko dai basu san suna dauke da cutar ba ko kuma ba a kai ga tattara bayanansu a kunshin rahoton WHO na shekarar 2021 ba.

A cewar jami’ar kasha 20 na sabbin kamuwa da cutar ta tarin fuka ko kuma TB na dauke da cutar HIV wanda ke matsayin babban tashin hankali lura da rashin kulawar da galibinsu ke fuskanta

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 24 minutes 8 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 5 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com