Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta jaddada buƙatar a ɗauki matakan gaggawa domin magance ƙaruwar hare-haren ta’addanci a tsakiyar Sahel.
Kwamishinan ECOWAS da ke kula da harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro, Ambasada AbdelFateh Moussa ne ya yi wannan kira a wani taron bayar da horo na yini biyar.
Read Also:
An yi wa taron taken Tabbatar da ci gaban zaman lafiya: Rawar ƴan sanda da jami’an Jandarma wajen tafiyar da ayyukan ECOWAS wajen wanzar da zaman lafiya.
ECOWAS ce ta shirya taron haɗin gwiwa da kwalejin horas da ƙananan jami’an soji ta Najeriya tare da tallafin shirin ECOWAS kan zaman lafiya da tsaro.
Moussa ya ce ayyukan wanzar da zaman lafiya da aka saba na zama tsohon yayi saboda yanayin rikici a yankin.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 13 hours 7 minutes 36 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 49 minutes 1 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com