Home SIYASA Kotu ta ce masu ƙalubalantar nasarar Tinubu su biya miliyan goma-goma

Kotu ta ce masu ƙalubalantar nasarar Tinubu su biya miliyan goma-goma

Babbar kotun tarayya da ke Abuja baban birnin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da yake yanke hukuncin ranar Talata, alƙalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya umarci masu ƙarar da kowannensu ya biya naira miliyan 10 ga ministan shari’a kuma Atoni janar na ƙasar.

Masu ƙarar dai na iƙirarin cewa shugaban ƙasar Bola Tinubu bai samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a baban birnin tarayyar Abuja, dan haka suke ganin bai cancanci zama shugaban ƙasar ba.

Mai shari’a Ekwo ya ce masu karar ba su da ‘yancin shigar da ƙarar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne kawai ya kamata a shigar da ƙasar, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp