Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).
An kaddamar da majalisar ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Sanata Kashim Shettima a zauren majalisar da safiyar ranar Alhamis.
A wani saƙo da Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce an ƙaddamar da majalisar ne a zaurenta da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja..
Read Also:
A Ƙwarya-ƙwaryar bikin ya samu halartar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume da gwamnonin jihohin ƙasar 36.
Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da majalisar, shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnonin su haɗa kai, wajen bunƙasa ƙananan hukumomi da ababen more rayuwa, duba da manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
“Ni da ku duk muna buƙatar hakan, kan haka muka gudanar da yakin neman zaɓukanmu, har ma muka yi rawa a gaban jama’a don jaddada alƙawuranmu, don haka, ba mu da dalilin yin korafi kan haka. ‘Yan Najeriya na nuna mana goyon baya. Suna son gyara kuma suna son hakan cikin gaggawa”.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 2 hours 59 minutes 27 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 4 hours 40 minutes 52 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com