Home General Sojoji sun hallaka ‘Yan Ta’adda 8 a jihar Kaduna

Sojoji sun hallaka ‘Yan Ta’adda 8 a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna tace sojoji sun hallaka ‘yan bindiga takwas a jihar dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar alhamis.

Yace sakamakon wani sumame da dakarun sojin suka kai yankin Kamfanin Doka, ne suka yi arba da ‘yan bindigar a yankin, nan suka hau musayar wuta ne sojojin suka sami nasarar hallaka bakwai daga cikin su.

“Ya yin da sojojin ke bincike a yankin sun sami nasarar bankado bindiga kirar AK47 guda uku, gami da gidan saka alburushi guda takwas, wanda suka kunshi hudu babu komai a cikin su sai kuma hudu dauke da alburusai 120 masu tsahon 7.62mm.” a cewar sa.

Aruwan ya kara da cewa sun kuma sami nasarar kwato kayayyakin da suka hadar da babu 6, wayoyin hannun uku, sai kuma radio kirar Baofeng, da kuma kayan fararen hula.

Haka kuma ya kara da cewa yayin da sojojin ke karkare atisayen sun sake yin wata arangamar da ‘yan ta’addan a yankin Gayam.

“Sojojin sun sami nasarar hallaka daya daga cikin su yayin da ake zargin sauran sun gudu da raunikan harbi a jikin su.” Kamar yadda ya bayyan.

Aruwana ya kara da cewa Gwamnan jihar Uba Sani ya yaba da kokarin dakarun bisa wannan nasara da suka samu a yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi sassan jihar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp