Mali ta sake dakatar da kafar talabijin mallakin Faransa TV5 Monde

Gwamnatin Sojin Mali ta dakatar da yaɗa shirye-shiryen gidan talabijin na TV5 a ƙasar har na tsawon watanni 3 bayan zargin tashar da yaɗa labaran rashin adalci a shirye-shiryenta sakamakon fitar da bayanai ba tare da jin dukkanin ɓangarorin da labarin ya shafa ba.

Tashar ta TV5 mai yaɗa shirye-shiryenta da harshen faransanci ita da kanta da sanar da wannan hukunci na mahukuntan na Mali ga kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sanarwar da Sojin na Mali suka fitar sun ce hukuncin zai fara aiki nan ta ke wato daga jiya 11 ga watan Stumban da muke ciki.

Hukumomin na sojin na Mali sun zargin wannan tashar da bada labarai da suka sabawa dokokin ƙasar.

Da samun wannan labari, kungiyoyi kare hakokin ƴan jarida ta kasa da kasa wato RSF da babbar murya ta na mai bayyana damuwa da kuma takaici ganin ta yada hukumomin sojin Mali suka aiwatar da wannan mataki ba tare da tuntuba ba.

Matakin shi ne na dakatar da watsa shirye-shiryen wannan tasha na tsawon watanni uku bisa zargin su da rashin daidaito a fannin yada labarai biyo bayan farmaki dakarun kasar a yankin Tinzaoutaene.

Hukumar Kula da Sadarwa ta kasar ta Mali (HAC) ta soki tashar ta TV5 Monde da bayar da rahoto a ranar 25 ga Agusta, a cikin labarun ta na Afirka, mutuwar akalla fararen hula goma sha biyar a harin da jirage marasa matuka a Tinzaouatène da ke arewacin kasar ta Mali.

Tashar ta TV5  a cikin wata sanarwa ta na mai nadama da kuma nuna mamakin ta na ganin hukumar kula da sadarwa ta kasar ta Mali ba ta nemi jin ko ta bakin masu wakiltar wannan tashar ba kafin daukar irin wannan mataki .

Ko a ƴan shekarun da suka gabata, ƴan lokuta bayan juyin mulkin sojojin kasar an dakatar da kafofin watsa labarai da yawa da kafafan yada labarai na France24 da kuma Radio France Internationale (RFI).

Haka zalika Sojin na Mali sun kuma dakatar da France2 a farkon shekarar 2024, kafin LCI ta fuskanci irin wannan makoma a karshen watan Agusta.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 10 hours 31 minutes 44 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 12 hours 13 minutes 9 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com