IKIRARI: wasu kafafe yada labarai sun ruwaito cewa tsohuwar minister Man Petir Allison Madueke, ta tabbatar da cewa ta bawa Dauda Lawan Dare. Gwamnan jihar Zamfara mai ci a yanzu ajiyar kudi sama da dalar amurka biliyan 9. A lokacin da yana babban daraktan bankin First Bank.
CIKAKKEN LABARIN: Wasu cikin kafafen yada labaran na kafara Internet sun yi ikirarin cewa tsohuwar minister Man Fetur lokacin Goodluck Jonathan, sun ambaci ce Diezani na cewa: “ni yanzu kamar kirista sabuwar haihuwa ce, kuma ina mataki na biyu na magani cutar kansa, kamar yadda likitana dan asali birtaniya ya bani shawarar na ci gaba da shan magani har karshen rayuwata.
“An zarge ni da wadaka da kudi a lokacin ina ministan Man fetur, kuma gaskiya ne na aikata abinda ake zargi na. don haka ina neman shugaban Nijeriya Bola Tinubu da ‘yan kasar su yafe min, su barni na dawo gida, na bayar da gudunmawa ta, saboda ita rayuwa abu ce mai sauyawa.”
Wasu manyan kafafen yada labaran irin su Sahara Reporters, This Nigeria da Business Day sun wallafa wannan labara, amma da wani salo da ban, inda suka bayyana cewa Uwar gida Madueke ta gana da ‘yan Jarida a birnin London bayan ta kai ziyarar dubu lafiyar ta. In suka rawaito ta na neman yafiyar Bola Tinubu da ke jagorantar Gwamnatin tarayya kasar.
Read Also:
Idan dai za’a iya tunawa Alison Madueke, tsohuwar minister Man fetir, ta bar Nijeriya zuwa kasar birtaniya kafin shugaba Jonathan ya mika mulki ga sabon shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015. Tun wancan lokaci, take fuskatanr binciken hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar ta’annati ta (EFCC) bisa zargin sace wasu kudi da suka kai dala amurka biliyan 2.59 a cikin dukar Nijeriya a lokacin tana ministan.
TABBATAR DA SAHIHANCIN IKIRARIN: domin tabbatar da sahihancin ikirarin da ke cewa Diezani Madueke ta bawa Dauda Lawal Dare, ajiyar kudi sama da dala biliyan 9, tawagar PRNigeria da ke yi binciken tabbatar da sahihancin labara ta gano mafi yawan kafafen yada labaran sun kawo labarin ba yada labarin ba kamar yadda hukumar ta EFCC ta wallafa a shafinta na sada zumunta ba, duk da cewa daga baya an goge.
Haka kuma PRNigeria ta yi yunkurin yin binciken ta hanyar yin amfani da (wayback machine) wata hanya ta yin binciken sahihancin labari, wadda ake amfani da iya ko da an goge abinda aka wallafa domin dawo da wallafar ta asali, saboda an goge abin da aka wallafa ashafin na EFCC.
Bayan da teburin binciken sahihancin labaran ya kara nitsawa wajen bincike, ya gano rabon da a ga tshuwar ministan a cikin jama’a tun lokacin da ta halarci kotun majistiri ta Westminster da ke London, a ranar litinin 2 ga watan oktoba 2023, ya yin sauraran karar da aka shigar gaban kotun bisa zargin cin hanci kamar yadda kafar reuters ta ruwaito
Amm kuma, a wata tattaunawa da tsohuwar minstar ta yi da kafara yada labarai ta Premium time ta musanta labarin da ke cewa ta gana da manema labarai a birninLondon, wanda ta ambaci sunan gwamnan jihar zamfara Dauda Lawan a ciki.
Ta bayyana labarin matsayin na “karya da kanzon kurege”
“Ban yi wata ganawa da manema labarai ba, kuma basu fadi koda Magana daya da ke da alaka da ni ba. Karya ce kawai da aka tsara da ni kai na ban san dalili ba”,
Kammalawa: PRNigeria ta yanke hukuncin cewa tsohuwar minister man fetur din, Allison Madueke, bata yi wata ganawa da manema labarai ba, wadda ta tabbatar da ta bayar da ajiyar kudin da suka haura Dalar Amurka Biliyan 9 ga Dauda Lawal Dare, gwamnana jihar Zamfara. Don haka Labarin ‘karya’ ne
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 18 hours 24 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 20 hours 5 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com