Home General Gwamnatin Kano za ta tallafawa matasa 3000 da wata kungiya ke koyawa...

Gwamnatin Kano za ta tallafawa matasa 3000 da wata kungiya ke koyawa sana’o’i a Kano – Sani Danja

Mashawarcin gwamnan Kano na musamman kan harkokin matasa da wasanni Sani Musa Danja ya sha alwashin hada kai da Kungiyoyi masu zaman kasansu don inganta rayuwar matasan jihar.

” Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya damu matuka da rayuwar matasa , shi yasa gwamnatinsa ta fi mai da hankali wajen tallafawa mata da matasa don inganta rayuwarsu, da ta al’umma baki daya”.

Alhaji Sani Danja ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda ake koyawa matasa 3000 sana’o’i daban-daban wanda wata kungiya mai suna 9ja food fiesta ya dauki nauyi a Kano.

Sani Danja ya baiwa matasan tabbacin gwamnatin jihar Kano zata tallafawa matasa da kayan aikin sana’o’in da suka koya ko jari, don tabbatar da cewa al’ummar Kano sun amfana da ilimin da suka koya.

Ya ce kofar ofishinsa a bude take don hada kai da duk wata kungiya mai son ganin ta tallafawa rayuwar matasan jihar Kano kamar yadda kungiyar 9ja food fiesta ta yi.

”Tun kafin na zama mai baiwa gwamnan Kano shawara akan harkokin matasa na damu matuka da al’amuran matasa da masu karin karfi domin talakawa da ya’yansu ne suke kallo fina-finai na har na kai matakin da na Kai, yanzu kuma da aikin da gwamna ya doramin , don haka dole na tsaya tsayin daka don ganin an inganta rayuwarku”.

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar 9ja food fiesta Muhammad Mustapha ya ce sun zo jihar Kano ne da nufin koyawa matasa maza da mata 2000 sana’o’i , amma daga bisani suka ga akwai bukatar kara adadin zuwa 3000 .

” Babu shakka wannan Aikin ne don tallafawa rayuwar matasan jihar Kano, kamar yadda muka yi a Abuja, amma mun ji dadin yadda mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin matasa da wasanni Sani Musa Danja ya ba mu duk wata gudunmawa da muke bukata don ganin an sami nasarar da muka sanya a gaba”.

Muhammad Mustafa ya yi kira ga kamfanoni da masu hannu da shuni a jihar Kano da su shigo cikin shirin don tallafawa matasan da suka gama koyon sana’o’in da jari ko kayan aikin da suka koya, don su dogara da kawunansu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp