Home General Majalisar dinkin Duniya ta zargi RSF da haifar da tarnaƙi a Sudan

Majalisar dinkin Duniya ta zargi RSF da haifar da tarnaƙi a Sudan

Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi mayaƙan rundunar RSF, da hana isar da kayan agaji yankin Darfur da ke fuskantar barazanar yunwa a Sudan da yaƙi ya ɗai-ɗaita.

A cikin wata sanarwa da jami’ar kula da ayyukan jin kai, ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Sudan Clementine Nkweta-Salami ta fitar, ta ce wasu dokoki da RSF ta sanya a yankin na Darfur, na haifar da tarnaƙi wajen gudanar da ayyukan ceton rayukan jama’a.

Dakarun na RSF da ke fafata yaƙi da sojojin Sudan tun a watan Afrelun shekarar 2023, sun kasance masu rike da ikon yankin na Darfur, musammann yadda su ka mamaye birnin El-Fasher da ke Arewacinsa a watan Mayun shekarar da ta gabata.

An dai ayyana ɓarkewar yunwa a wasu yankuna biyar na Arewacin Darfur, kuma ana zaton ta ƙara bazuwa zuwa wasu yankuna biyar nan da watan Mayu mai zuwa.

A cewar wasu alkaluma da wata ƙungiya da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, sun nuna cewa kimanin mutum miliyan 7 ne ke fuskantar yunwa a yankin na Darfur.

A cewar wasu alkaluma da wata ƙungiya da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, sun nuna cewa kimanin mutum miliyan 7 ne ke fuskantar yunwa a yankin Darfur.

Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta buƙaci RSF ta sauƙaƙa dokokin da ta sanya a yankin, don bada damar isar da kayan agaji ga al’ummar da ke cikin tsananin buƙata.

Shi dai yaƙin na Sudan ya lakume rayukan ɗaruruwan mutane, ya kuma raba sama da mutum miliyan 12 da muhallansu, sannan akwai wasu kimanin miliyan 25 da ke fuskantar barazanar yunwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp