Home DUNIYA Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴanta’adda a Jihar Taraba

Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴanta’adda a Jihar Taraba

Sojojin Najeriya karkashin dakarun  Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun sanar da kashe ƴanbindiga uku, sannan suka lalata mazauninsu tare da ƙwace makamai a ƙaramar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.

Sojojin sun samu nasarar ce a ranar 5 ga Afrilu, kamar yadda kakakin sashen Olubodunde Oni ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa da sojojin suka isa yankin Chibi, sai ƴanbindigar suka fara tserewa, “inda sojojin suka bi sahunsu suka yi musayar wuta, inda dakarunmu suka kashe ƴanbindigar guda uku, sannan suka tarwatsa mazauninsu, tare da ƙwato makamai.”

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na Najeriya sun yi sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle a kwanakin baya, inda suka tarwatsa mazaunan ƴanbindiga da dama.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp