Home General Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya a Borno

Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya a Borno

Mayaƙan Boko Haram sun ƙaddamar da farmaki kan sansanin sojin Najeriya da ke Ƙaramar Hukumar Marte a jihar Borno, inda suka kashe wani adadi na sojojin da ba a bayyana ba.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da harin wanda aka kai da misalin karfe 3 na safiyar wannan Litinin kan sansanin sojin na Forward Operation mai ɗauke da bataliya ta 153 kamar yadda jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriyar ta rawaito.

Ɗaya daga cikin majiyoyin da ya buƙaci sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa, mayaƙan na Boko Haram sun kuma yi garkuwa da wasu sojojin na Najeriya bayan sun raba su da muhallansu a yayin farmakin.

ISWAP ta karɓe iko da Marte, sun kashe wani adadi na sojoji, sun kuma yi garkuwa da wasu, wasu da dama sun tsere zuwa Dikwa, kuma yanzu haka suna samun mafaka a sansanin runduna ta 24 da ke Dikwa

Ƴanta’addar sun kona tankunan yaƙi tare da awon gaba da tarin makamai daga sansanin sojin a cewar majiyar tsaron.

Ƙaramar Hukumar Marte dai, na da tazarar kilomita 38 daga Ƙaramar Hukumar Dikwa a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya

Wata majiya a Dikwa ta shaida wa Daily Trust cewa, an jiyo ƙarar harbe- harbe

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp