Bincike: Shin da gaske ne Sojojin Nijeriya sun fi bawa shanu tsaro maimakon Al’umma a Yelewata, dake Jihar Benuwai Kamar Yadda Wani Bidiyo ya Nuna?
Ikirari: Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumuntana zamani, musamman a dandalin Facebook, Instagram da manhajar WhatsApp, yana zargin cewa dakarun sojojin Nijeriya na bawa shanu tsaro a garin Yelewata da ke jihar Benue, a madadin su kare rayukan al’umma.
Ta cikin bidiyon an ji wata murya da harshen Pidgin na cewa: “See how Army de guide NAMA for Fulani and they no fit guide Benue people.” wato kalli yadda sojoji ke gadin Nama (shanu) ga fulani, amma sun kasa kare jihar benuwai, Wata murya kuma, mai kama da ta dan jarida da ke rike da makirufo mai tambarin CCC News, ta ce: “The security the locals couldn’t get is what cows are getting.” Ma’ana dai tsaron da al’umma suka gaza samu shi shanu ke samu.
Bidiyon ya nuna wasu shanu a kan titi, inda wasu mutane sanye da kayan soji da hula kore suke zagaye da su, tare da wasu matasa da ma ‘yan kallo. A bango, wani allon rubutu na nuna cewa wurin da abin ke faruwa shi ne Yelewata, a jihar Benuwai.
Bidiyon ya haifar da cece-kuce sosai a yanar gizo, inda mutane da dama ke caccakar abin da suka kira fifita dabba kan rayukan dan Adam.
Jihar Benuwai ta dade tana fama da rikicin manoma da makiyaya, wanda ya haddasa asarar rayuka da raba mutane da muhallansu. Wannan rikici na yawan haifar da labaran karya da kanzon kure gami da yada bidiyo masu tayar da hankali a kafafen sada zumunta.
Read Also:
Tabbatar da Sahihancin Ikirari: Tawagar bincike ta PRNigeria ta gudanar da sahihi kuma ingantanccen bincike domin gano sahihancin bidiyon da kuma ikirarin da ke cikin sa.
Bincike ya nuna cewa bidiyon ya fara yaduwa tun ranar 18 ga Yuni, 2025, inda ya karade shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp.
Ta hanyar amfani da kayan bincike irin su InVID da Deepware, PRNigeria ta gano cewa bidiyon na dauke da alamun karya ta hanyar fasahar zamani. An lura da motsin da bai dace ba daga shanu da mutanen da ke cikin bidiyon, wanda ke nuni da cewa an kirkiri bidiyon ne ta hanyar fasahar deepfake. Deepware ta tantance bidiyon da kashi 98% cewa an samar da da shi ta kirkirarriyar fasahar AI ne.
Binciken hoto ya kuma nuna cewa kayan sojin da ke jikin wadanda aka ce sojojin Nijeriya ba su yi daidai da na rundunar sojin kasar ba, haka kuma hulunansu ba irin na soja ba ne. Fuska da inuwa da sauran abubuwa masu alaka da haske da motsi sun nuna gazawar hoton na kasancewarsa hoton gaskiya, wanda ke daga cikin alamomin bidiyon da aka kirkira.
Haka kuma, babu wata jarida ko kafar yada labarai mai inganci da ta ruwaito wannan lamarin, kuma rundunar sojin Nijeriya ba ta bayyana komai a hukumance game da wannan bidiyo ko zargin kare shanu ba.
Kammalawa: Bayan cikakken bincike, PRNigeria ta tabbatar da cewa bidiyon da ake yadawa yana nuna cewa sojojin Nijeriya na kare shanu a jihar Benue ba gaskiya ba ne. Bidiyon kirkirarre ne da aka hada ta hanyar fasahar zamani (AI) da nufin tada tarzoma gami da rudani a cikin al’umma.
Hukunci: Ikirarin da aka yi kan sojojin Nijeriyar kayar ce!
Ikirarin cewa sojojin Nijeriya na kula da shanu a Benue kamar yadda aka nuna a bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne. Bidiyon an kirkire shi ne da fasahar AI kuma bai wakilci wani abu da ya faru a gaskiya ba.
PRNigeria.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1496 days 20 hours 9 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1478 days 21 hours 51 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com