Bincike: Shin da gaske ne an kama wani mutum da ya shiga cikin rufin Silin a bankin FCMB domin yin kutse?

Ikirari: Wani da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta na zamani, musamman a manhajar X, wanda ke nuna cewa an kama wani matashi da ke kokarin yin kutse a kwamfutocin bankin FCMB wato (First City Monument Bank) bayan ya kwashe tsawon dare boye cikin rufin silin din bankin.

Rubutun da aka hada a jikin bidiyon na cewa: “Wannan Abokin huldar bankin FCMB ne a jiya, in da ya shiga bayan gida kaitsaye ya rufe kansa a ciki, sai ya shiga cikin silif. Bayan da ya fahimci dukkan ma’aikatan sun tafi sai ya fito domin ya yi kutse cikin kwamfutocin bankin….. da safiyar nan, bayan da abokan aikina suka zo, sai suka fahimci kofara a rufe take ta ciki. Suka kuma yi kokarin karya kofar daga nan ne suka lura da wani mutum a cikin silif din. Da sauri bayan sun kunna kwamfutocin sai suka ga ta rubuta cewa ‘Restarting, click OK to accept.’”

Bidiyon ya ya mutsa hazu a kafar internet, wanda ya haifar da kace-nace kan tsaron bankuna, tattalin arziki, da kuma jami’an ‘yansanda. Jama’a da dama sun nuna damuwarsu matuka, wadanda wasu kuma suka dora alhakin faruwar lamarin da gazawar jami’an tsaro da suka bari hakan ta faru.

Bankin (FCMB) na daga cikin manya kuma sannannun wurin ajiyar kudi da hada hadar su a fadin Nijeriya. Wanda yake samarwa da miliyoyin mutane kasar harkokin bankin na zamani.

Binciken Sahihancin Ikirarin: domin tabbatar sahihancin ikirarin  PRNigeria ta gudanar da binciken sahihancin labara da wasu haruffa da kafar sada zumunta na zamani.

Binciken mu ya nuna mana cewa bidiyon ya yado ne a makon farko na watan Yuni 2025, wanda cikin dan kankanin lokacin ya tara makallata a mabambanta kafafen sada zumunta.

Bayan fadada binkice an gano lamarin ya auku a bankin na FCMB dake yankin Owerri, babban birnin jihar Imo. Mutumin, wanda har yanzu ba’a bayyana ko waye ba, ya samu damar kutsawa cikin harabar bankin inda ya fake cewa shi abokin huldar bankin ne a lokacin aiki. Sai ya shiga bayan gida ya rufe kan shi a bayan gida, inda  ya shiga cikin silif, domin jiran har sai an tashi daga aiki domin samun damar yin kutse a cikin kwmafutocin bankin.

Kafafen yada labarai na gida da shafukan shaidun gani da ido sun bayyana cewa yayin da ma’aikatan bankin suka dawo aiki da safe, sai suka fahimci cewa bayan gida a rufe yake daga ciki. Sai suka yi amfani da karfi domin kaya kofar shiga bayan gida, nan ne suka lura da wani mutum a cikin silif. bayan sun kunna kwamfutocin sai suka ga sun rubuta cewa ‘Restarting, click OK to accept.’”

‎bayan da aka kira jami’an tsaro sai domin kama wanda ake zargin. Haka kuma wani yankin na bidiyon ya nuna yadda ake cikinzarafin sa, wanda hakan ya ja hankalin al’umma wanda uksa kalubalanci hukumar ‘Yansanda.

Da yake martani kan bidiyon, kakakin rundunar ‘Yansanda Nijeriya CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana yadda jami’an suka gudanar da aikin matsayin rashin kwarewa, ya kuma tabbatar da cewa za su gudanar bincike.

“ rashin kwarewa ne wannan. Abin da ya auku a cikin bidiyon ba daidai bane. Kuma za mu duba domin gudanar da bincike,” Adejobi kamar yadda ya bayyana X.

Kawo lokacin hada wannan bincike banki FCMB bai fitar da wata sanarwa ta musamman kan lamarin ba, sai dai a wasu shafukan bankin ya gargadi abokan huldarsa da su lura da asusun ajiyarsu su kuma guji bayyana kwanan watan haihuwarsu, da wasu lambobin sirrinsu ga kowa.

Kammalawa:

Bayan gudanar da bincike, PRNigeria ta gano cewa wannan ikirarin da aka yi gaskiya ne. an sami wani mutum a cikin rufin silif a cikin dare a bakin FCMB dake Owerri a jihar Imo, wanda ya yi kokarin yin kutse a kwamfutocin banki. An kama shi kuma mika shi hannun ‘Yan sanda.

Hukunci: Ikirarin Gaskiya ne

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 5 hours 3 minutes 22 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 6 hours 44 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com