Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon rikici – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda yunwa ke kara kamari a arewa maso gabas na Najeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda fiye da mutane miliyan 3.7 ke fuskantar matsananciyar rashin abinci.

A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa.

A Dikwa, manoma na tashi da safe su ratsa tafiya mai tsawo domin yin noma na ‘yan awanni kafin su koma gida.

Churi Ibrahim, wani tsohon manomi dan shekara 70 da ke ciyar da iyalinsa goma, ya ce farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi, kuma kudin ɗinki da yake samu da dare bai isansu.

Modu Umar, wani shugaban al’umma, ya bayyana cewa yunwa tana haddasa cututtuka kamar gudawa a cikin yara da manya saboda rashin abinci da magani.

“Mutane na fita nesa su tara itace domin samun kudin siyan abinci.” in ji shi.

ICRC dai ta ce ta fara wani shiri na taimakawa noma ta hanyar raba iri da kayan aikin noma ga sama da iyalai 21,000 a bana, domin tallafa musu a lokutan kaka da rani.

“Ana kuma shirin rarraba famfunan ban-ruwa masu aiki da hasken rana domin noman rani.” in ji ƙungiyar ICRC.

Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta ce ana fargabar lokacin Ƙarancin abinci daga Yuli zuwa Satumba, inda mutane ke buƘatar sayen abinci, amma Ƙarancin kudi yana hana su cika buƙata.

Wata uwa mai yara biyar, Bintu Konto, ta ce: “Wasu lokuta muna kwana da yunwa har kwana biyu zuwa uku. Idan Allah ya kawo wani abu, sai mu ci.”

Ƙungiyar ICRC na aiki a Borno tun 2012 inda take taimakawa al’ummomin da rikici ya shafa da kuma kare martabar fararen hula bisa dokokin Geneva na 1949.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1495 days 7 hours 3 minutes 54 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1477 days 8 hours 45 minutes 19 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com