Home SIYASA SIYASA: Kwankwaso Yayi Murabus

SIYASA: Kwankwaso Yayi Murabus

Kwamishinan Ma’aikatar Raya karkara ta Jihar Kano Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya ajiye mukamin sa na Kwamishina, sa’oi bayan gwamnan jihar ya bukaci hakan ga masu muradin tsayawa Takara cikin jami’an gwamnatin.

Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso yace ya ajiye mukamin nasa ne domin yana da sha’awar yin takarar Dan Majalisar wakilai dake wakiltar Kananan Hukumomin Kura, Madobi da Garun Mallam a zauren majalisar wakilai a zabe mai zuwa, kamar yadda guda cikin hadiman sa Musa Dan Zariya ya shaidawa PRNigeria Hausa ta wayar tarho.

Tsohon Kwamishinan yace “Ina fatan Zan Zama Dan takarar Majalisar wakilai da zai wakilci Kananan Hukumomin Kura Madobi da Garun Mallam a jam’iyyar APC.

Tuni kwamishinan Ruwa na Jihar Kano Sadiq Wali yayi murabus daga kujerar sa, inda ya sayi Fom din takarar Gwaman jihar Kano a Jam’iyyar PDP.

Idan za’a iya tunawa a safiyar lahadi wani rahoto ya bayyana yadda gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje na bada Umarni ga Masu rike da mukamai a gwamnatin Kano dasu ajiye mukamansu Matukar suna da sha’awar tsayawa takara a zabe Mai Zuwa.

Umarnin daya yi dadai da sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yiwa gyaran fuska.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp