Home SIYASA Gwamnonin Arewacin Nijeriyar sun yi Fatali Da Zabin Lawan Matsayin Dan Takarar...

Gwamnonin Arewacin Nijeriyar sun yi Fatali Da Zabin Lawan Matsayin Dan Takarar APC

Ta cikin wata ganawa da sukayi da shugaban kasa muhammadu Buhari, Gwamnonin, sun jaddada aniyar sun a mayar da mulkin Kudancin kasar a shekarar 2023

Shugaban kungiyar Gwamnonin kuma gwamnan jihar Plateau Simon lalong, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan ganawar a fadar shugana kasa dake Villa a babban birnin tarayyar Nijeriya, inda yace shugaba Buhari ya tabbatar musu cewa bai goyi bayan wani mutum ba cikin mutum 23 da ke son jam’iyyar ta tsayar da su Takara.

Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce sun dauki matakin goyon bayan dan takara daga kudancin kasar ne domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasar.

Dambarwar da ake yi kan batun dan takarar shugaban kasar na Najeriya a jam’iyyar APC ta sa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwa yana nesanta kansa ga goya wa kowanne dan takara baya.

Wannan kuma na kunshe ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai inda ya ambato Shugaba Buhari yana cewa babu wanda ya zaba a matsayin dan takarar APC na shugaban kasa a zaben 2023.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp