APC ta bayyana sunayen wadanda ta ke so su zama shugabannin majalisar Majalisa ta 10

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta amince da rabon mukamai na shugabancin majalisa ta 10.

Ta ce ta amince da Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattijai daga shiyyar Kudu maso Kudu.

Haka zalika, Sanata Barau Jibrin zai kasance mataimakin shugaban majalisar dattijai daga Arewa maso Yamma.

Wata sanarwa da jam’iyyar mai mulki ta fitar, ta ambato kwamitin gudanarwa na APC yana cewa matakin ya zo ne bayan rahotannin tuntuba da tarukan da jam’iyyar ta yi da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Da kuma shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki game da rabon mukamai zuwa shiyyoyi daban-daban na kasar game da jagorancin majalisa ta 10.

A Majalisar Wakilai kuma, APC ta ce tana goyon bayan Hon Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalisar ta wakilai daga Arewa maso Yamma.

Sai Ben Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar wakilai daga Kudu maso Gabas.

Sanarwar ta ce Kwamitin Gudanarwar APC na Kasa ya lura cikin mutuntawa da sakamakon taruka tsakanin zababben shugaban kasa da shugabancin kwamitin.

Wannan mataki ya tabbatar da rade-radin da aka dade ana yi cewa APC ta bai wa Sanata Godswill Akpabio matsayin shugaban majalisar dattijai da kuma Abbas Tajuddeen matsayin shugaban majalisar wakilai da za a bude a nan gaba.

Da wuya a iya sani zuwa yanzu, ko wannan mataki na jam’iyyar mai mulki, zai kawo karshen dambarwa da kai ruwa-ranar da ake yi game da neman shugabancin majalisa ta goma.

Sai a watan Yuni ne za a kaddamar da sabuwar majalisar, wadda za ta yi aiki kafada da kafada da zababben shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu. A baya, zaben shugabannin majalisun tarayya ya saba zuwa da zafi, da kuma nuna bijirewa ga shugabancin jam’iyya mai mulki da kuma bangaren zartarwa.

Ko a majalisa ta takwas a shekara ta 2015, ‘yan majalisar dattijai sun bijirewa umarnin jam’iyyar APC mai mulki, inda suka zabi Sanata Abubakar Bukola Saraki, matsayin shugabansu a kan dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Ahmad Lawan.

Yayin da majalisar wakilai ta zabi Yakubu Dogara, maimakon Femi Gbajabiamila, dan takarar da jam’iyyar ta goyi baya a lokacin.

Lamarin dai ya janyo zaman doya da man ja a wa’adin farko na jam’iyyar APC, bayan ta kwace mulki daga hannun PDP.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1191 days 2 hours 23 minutes 28 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1173 days 4 hours 4 minutes 53 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com