Home SIYASA Sanata Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattijai ta goma

Sanata Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattijai ta goma

Sanata Godswill Akpabio ya yi nasarar zama Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya ta goma, bayan zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dattijai sun kaɗa ƙuri’a.

Akawun majalisar tarayya, Sani Tambuwal ne ya bayyana sakamakon zaɓen da ‘yan majalisar suka yi, inda ya ce Sanata Godswill Akpabio ya yi nasara da rinjayen ƙuri’a 63.

Ya dai kayar da abokin fafatawarsa, Sanata Abdul’aziz Yari ne wanda ya samu ƙuri’a 46.

Tuni Akawu Sani Tambuwal ya rantsar da sabon Shugaban Majalisar Dattijan, bayan ƙuri’un da ‘yan majalisa 107 suka kaɗa da safiyar Talata.

Matakin ya zo ne jim kaɗan da buɗe zaman majalisa ta goma a ranar Talata.

Magoya bayan sabon shugaban majalisar dattijan sun yi ta sowa a zauren majalisar inda suka je suna rungume Sanata Godswill Akpabio.

Da kammala zaɓen sabon shugaban majalisar dattijain kuma, yanzu an shiga matakin zaɓen mataimakinsa, inda Sanata Godswill Akpabio ya ɗare kan kujerar shugaban majalisar dattijai

Akawun Majalisar Dattijai ya ayyana Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattijai ta goma

Daga bisani, akawun majalisa ya rantsar da Sanata Barau Jibrin a matsayin halastaccen mataimakin shugaban majalisar dattijai.

Akpabio da Barau su ne ‘yan takarar da jam’iyyar APC mai mulki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka mara wa baya don zama shugaban majalisar dattijai da mataimakinsa.

Tuni dai, akawun majalisar dattijai ya shiga rantsar da zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dattijan.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp