Gwamnan jihar Ondo Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya mika sunayen mutane shida ga majalisar dokokin jihar domin tantancesu matsayin sabbin kwamishinonin jihar.
sunayen da gwamnan ya mika sun hadar da:
1. Mrs. Omowumi Isaac, ACCA
2. Mr. Olukayode A. Ajulo, SAN, OON
3. Engr. Razaq Obe
4. Pastor Emmanuel Igbasan
5. Barrister Akinwumi Sowore
6. Mr. Oseni Oyeniyi
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
haka kuma gwamnan ya amince da nadin wasu mutun uku matsayin masu bashi shawara na musamman da suka hadar da:
1. Hon. Olugbenga Omole, matsayin mai bayar da shawarar na musamman kan harkokin kwarewa da samar da bayanai.
2. Mrs. Olamide Falana, matsayin mai bayar da shawara na musamman kan jinsi
3. Mr. Alabi Johnson, sai mai bayar da shawara na musamman kan makamashi.
PRNigeria Hausa












