Hukumar Alhazai ta kasar nan ta ce kawo yanzu ta kwashe maniyyatan aikin hajjin bana 10,675 daga kasar zuwa kasa mai tsarki.
Read Also:
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan harkokin yada labarai ta hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, inda tace sun sami nasarar jigilar Maniyyata 4,665 ta jirgin FlyNas, sai jirgin Max Air da ya kwashe maniyyatan 4,479 jirgin Air Peace ya yi jigilar 1,531.
Ta kara da cewa kawo yanzu dai hukumar bata sami rahoton wani jirgi da aka soke tashin sa sai dai jirgin maniyatan jihar kwara da aka daga tashin sa a daren talata.
Haka kuma jihar Nassarawa ta zama jiha ta farko data fara kamala jigilar maniyyatan ta kimanin 1,794 na shekarar 2024 haka kuma jihar Oyo da rundunar sojoji ake sa ran zasu kamala jigilar zuwa dare.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 24 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 5 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com